Kano: 'Yan Sanda sun kama masu adaidaita dake kwacewa fasinjoji waya

Kano: 'Yan Sanda sun kama masu adaidaita dake kwacewa fasinjoji waya

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi ram da wasu matasa biyu da ake zargi da kasancewa barayin waya ne dake yawo a adaidaita sahu
  • Kamar yadda Abdullahi Kiyawa, kakakin rundunar ya sanar, sun bayyana cewa suna aika-aikarsu a State road, Tukur Road da Zaria road inda suke kwacen wayoyi ga fasinjoji
  • Matasan biyu suna tuka adaidaita ta haya amma ana nisa sai su kwace wayoyin fasinjoji, sun kai shekara daya suna wannan barnar a Kano

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wasu barayi biyu dake basaja matsayin matukan adaidaita sahu inda suke yi wa mutane fashin wayoyinsu.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana wannan a bidiyon da ya fitar ranar Litinin 4 ga watan Yuli, yace daya daga cikin wadanda ake zargin tsohon mai laifi ne.

Barayin wayoyi
Kano: 'Yan Sanda sun kama masu adaidaita dake kwacewa fasinjoji waya. Hoto daga Abdullahi Kiyawa
Asali: Facebook
"A ranar 20 ga watan Yunin 2022, mun samu rahoton cewa wasu barayi suna basaja matsayin matukan adaidaita sahu, suna kwace wayoyin fasinjoji a kan titin gidan gwamnati, titin Tukur da titin Zaria a Kano. Suna amfani da adaidaita mai lambar KAROTA KBY 0126," yace.
"Bayan samun rahoton, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Sama'ola Shu'aibu Dikko, fsi, ya tada tare da umartar jami'an rundunar Puff Adder karkashin jagorancin CSP Bashir Musa Gwadabe domin bibiya tare da kamo masu laifin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Da gaggawa tawagar ta fada aiki. Kokarinsu ta hanyar bayanan sirri ya kai su ga kama Mohammed Jidda mai shekaru 20 da Adamu Sulaiman mai shekaru 22 dukkansu mazauna kwatas din birged dake Kano.
"An kama wadanda ake zargin a titin gidan gwamnati a ranar 25 ga watan Yunin 2022 a adaidaita sahu dauke da wayoyi uku da ake zargin na sata ne.

"A yayin bincike, wadanda ake zargin sun amsa cewa su barayi ne da suka kware wurin amfani da adaidaita sahu wurin kwace wayoyin fasinjoji.

"Dukkansu sun tabbatar da suna amfani da kwayoyi kuma suna aika-aikarsu a kan titin Tukur, titin gidan gwamnati, titin Zaria da sauran wurare a kwaryar birnin Kano na sama da shekara daya. Wayoyin da aka samu daga wurinsu duk sun sace su ne daga fasinjoji.
"An gano masu wayoyin. Daya daga cikin wadanda ake zargi mai suna Mohammed Jidda ya bayyana cewa an taba kama shi da irin laifin, aka kai shi kotu kuma aka yanke masa hukuncin wata shida a gidan yari ko kuma tara. Ya yi wata uku a gidan amma daga bisani an biya tara kuma aka sake shi."

A daya bangaren, kwamishinan 'yan sanda ya umarci tsananta bincike wanda bayan nan za a mika wadanda ake zargin gaban kotu domin yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel