An hana matar Ekweremadu ganinsa yayin da yaransu suka bayyana a kotu

An hana matar Ekweremadu ganinsa yayin da yaransu suka bayyana a kotu

  • Kotun Majistare da ke a kasar Birtaniya ta hana Beatrice, matar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ganinsa yayin da ya gurfana a gabanta
  • A yayin zaman yau Alhamis, 30 ga watan Yuni, Beatrice ta nemi kotu ta bata damar bayyana a gefensa saboda bata sanya shi a ido bat un makon jiya
  • Sai dai kuma, kotun ta ki amsa bukatar matar Ekweremadu sannan kuma ta ki bayar da belinsa kasancewarsa babban mutum mai fada aji

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Birtaniya - Jaridar Daily Post ta rahoto cewa an hana Beatrice, uwargidar tsohon shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, ganinsa a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, lokacin da dan majalisar ya gurfama a gaban kotun Majistare ta Birtaniya kan tuhumar da ake masa da ya shafi cire sassan jikin mutum.

Kara karanta wannan

Lauya Mai Addinin Gargajiya Ya Sake Zuwa Kotu Da Kayan 'Bokaye'

A yayin zaman na yau, Beatrice ta bukaci kotu da ta bari ta gurfana a gefen mijinta saboda basu ga junansu ba tun bayan zaman karshe da aka yi a makon jiya.

Sai dai kuma, kotun ta ki amsa bukatar tata sannan kuma ta ki ba Ekweremadu beli.

Ekweremadu
An hana matar Ekweremadu ganinsa yayin da yaransu suka bayyana a kotu Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa an tsare Ekweremadu ne saboda kotun ta bayyana cewa shi babban mutum ne mai fada aji, kuma shari’ar na da alaka da karamin yaro da kuma bautarwar zamani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yaran tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan su biyu sun kasance a kotun a lokacin da mahaifinsu ya sake gurfana a yau Alhamis.

Lamarin na zuwa ne awanni 24 bayan shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta yo hayar lauyoyi don kare ahlin Ekweremadu.

Lawan ya kuma sanar da cewa wata tawaga za ta gana da su Ekweremadu a Landan kan shari’ar.

Kara karanta wannan

Kogi: Tanka Dauke da Man Fetur Tayi Bindiga, Ta Halaka Rayuka 3 a Lokoja

Matsalar Ekweremadu ta fara ne lokacin da ya yi kikarin samawa yarsa da ke fama da rashin lafiya gudunmawar koda.

A cewar yan sanda masu kara, tsohon mataimakin Shugaban majalisar dayyawan ya kawo karamin yaro daga Najeriya a kan wannan lamarin.

Sanata Ekweremadu ya bayyana gaban Kotun Birtaniya

Mun dai kawo cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, ya bayyana a gaban Kotun Majistire da ke a ƙasar Birtaniya kan tuhumar da ake masa na yanke sassan jiki.

Channels tv ta ruwaito cewa mai gabatar da ƙara ya yi ikirarin cewa David Ukpo, wanda ake zargin tilasta masa aka yi ya ba ɗiyar Sanatan ƙoda, bai wuce shekara 15 ba a duniya.

Sai dai an ɗage zaman sauraron ƙarar zuwa ranar 7 ga watan Yuli, 2022 domin baiwa Antoni Janar na Birtaniya, Suella Braverman, damar yanke ko za'a cigaba da sauraron karar a ƙasar ko a maida ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Kotu ta ki Sauraron Shari'o'in Lauyan da Yayi Shigar Bokaye Zuwa Kotu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng