Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira birnin Lisbon, kasar Portugal
- Shugaba Muhammadu Buhari ya isa kai ziyarar aiki kasar Portugal bisa gayyatar Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa
- Yayin ziyarar aikin, za a karrama Shugaba Buhari da lambar yabo ta ‘Great Collar of the Order of Prince Henry’
- Buhari zai gana da farai ministan kasar, Antonio Costa, shugaban majalisa Dr Augusto Santo Silva da yan Najeriya mazauna Portugal
Lisbon - Shugaba Muhammadu Buhari dira Lisbon, babb birbirnin kasar Portugal lafiya a ranar Talata, 28 ga Yunu, 2022.
Buhari Sallau, hadimin shugaban kasan ya bayyana hakan a gajeren jawabi da hotunan da ya fitsr a shafinsa na Facebook.
Yace:
”Shugaba Muhammadu Buhari ya isa Lisbon, Portugal don ziyara tare da halartar taron teku na majalisar dinkin duniya.”
Kalli hotunan:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wadanda za su yi wa Buhari rakiya
Wadanda za su raka Buhari a tafiyar sun hada da Ministan Harkokin wajen Najeriys, Geoffrey Onyeama; Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed; Ministan Masana'antu, Kasuwanci da Saka Hannun Jari, Adeniyi Adebayo; Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare da Ministan Sadarwa da Tattalin arzikin zamani, Isa Pantami.
Saura sun hada da NSA, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya); Direkta Janar na NIA, Amb. Ahmed Rufa’i Abubakar da Shugaban NiDCOM Honorable Abike Dabiri-Erewa.
Asali: Legit.ng