Ekweremadu: Takardar haihuwar matashin da zai bayar da koda ya nuna shekarunsa 21 ba 15 ba – Hukumar NIS
- Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta ce matashin nan da ake zargin Ike Ekweremadu sun kai Birtaniya domin a cire masa koda ba yaro ba ne
- A cewar hukumar, takardar haihuwar da David Ukpo ya gabatarwa hukumar a yayin rijistar fasfo da shaidar NIN dinsa sun nuna shekarunsa 21 ba 15
- A ranar Alhamis da ta gabata ne aka kama tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan, Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice a Ingila
Abuja - Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta bayyana cewa shekarun David Ukpo, 'mai bayar da gudummawar koda' wanda ke tsakani a zargin da ake yiwa Sanata Ike Ekweremadu na yunkurin cire sassan jiki, 21 ba 15 ba.
Kakakin hukumar NIS, Amos Okpu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Lahadi, 26 ga watan Yuni, bayan wata hira da yan jarida.
Okpu ya ce takardar haihuwar da Ukpo ya gabatar a yayin rijistar neman fasfo dinsa ya nuna cewa shekarunsa 21, jaridar The Cable ta rahoto.
An tsaresu su biyun har zuwa ranar 7 ga watan Yuli yayin da bincike ke ci gaba da gudana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga bisani an rahoto cewa sanatan ya aikawa babban hukumar Birtaniya rubutacciyar takarda a kan haka.
Koda dai hukumomin 'yan sandan Birtaniya dai sun ce shekarar matashin 15, takardar fasfo dinsa da na bankinsa ta nuna shekararsa 21.
Ya kara da cewa takardar shaidar haihuwar Ukpo ya nuna an haife shi a ranar 12 ga watan Oktoba, 2000 wanda ke nufin zai cika shekaru 22 a watan Oktoban 2022.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Gaskiyar al’amarin da ya shafi shari’ar da ke sama, shi ne, Mista David Ukpo Nwamina ya nema sannan ya biya kudin fasfo ta shafin NIS sannan bayan nan ya je ofishin fasfo na Gwagwalada, Abuja, a ranar 2 ga watan Nuwamban 2021 don yi masa tambayoyi.
“Don marawa bukatar tasa baya, Mista Nwamina ya gabatar da dukkanin takardun da ake bukata, ciki harda takardar haihuwarsa, wanda ya nuna an haife shi a ranar 12 ga watan Oktoban 2000, takardar shaidar dan kasarsa ta yi daidai da na haihuwarsa.”
Da aka tambaye shi ko gwamnatin Burtaniya ko majalisar dokokin kasar sun tuntubi ofishin kula da shige da fice game da batun David, sai ya ce babu wanda ya tuntubi hukumar, jaridar Vanguard ta rahoto.
Zargin Cire Sassan Jikin Mutum: Sanatoci Suna 'Tare Da Ekweremadu', In Ji Smart Adeyemi
A gefe guda, dan majalisar tarayyar Najeriya, Sanata Smart Adeyemi ya ce sanatoci ba za su yi watsi da Sanata Ike Ekweremadu ba kuma wasu cikinsu na kokarin tuntubarsa.
Yana martani ne kan zargin cire sassan jikin mutum da aka yi wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan.
Asali: Legit.ng