Jarumin maigida ya dumfari dan bindiga yayinda yake kokarin yiwa matarsa fyade

Jarumin maigida ya dumfari dan bindiga yayinda yake kokarin yiwa matarsa fyade

  • Magidanci ya cire tsoro ya kwace bindiga hannun barawo yana kokarin yiwa matarsa fyade
  • Dan bindigan ya yi kokarin zakkewa matar mutumin a gabansa bayan kwashe musu kudi
  • Ana zargin mahaifiyarsa da tayashi aikata harkar fashi da makami ta hanyar yi masa ajiyar kayan sata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Hukumar yan sandan jihar Ondo a ranar Laraba ta bayyana cewa ta damke yan bindiga masu tada kayar baya guda 14 a fadin jihar.

Yan ta'addan sun hada da Ojo Rotimi, Tosin Omoniyi, Jimoh Dele, Uwanfor Destiny, Babajide Moses, Tope Gbenga, John Simeon, Akinniranye Blessing, Jude Stephen da Iranlowo Ayomide.

Daya daga cikinsu an damkeshi ne yayinda yake kokarin yiwa matar aure fyade bayan musu fashi da makami a gidansu dake garin Idanre, karamar hukumar Idanre ta jihar.

A cewar yan sanda, dan fashin ya shiga ta taga misalin karfe daya na dare kuma ya kwace musu kudade da wasu dukiya, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Mai Wakar Zazu, Portable Ya Saduda Ya Mika Kansa Hannun Yan Sanda a Ogun

Barawo
Jarumin maigida ya dumfari dan bindiga yayinda yake kokarin yiwa matarsa fyade Hoto: MobilePunch
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mrs Funmilayo Odunlami, ta bayyana cewa:

"Yayinda yake kokarin yiwa matar fyade gaban mijinta ne shi mijin yayi ta maza ya dira kansa, ya damke shi kuma ya kwace bindigarsa tare da taimakon makwabtansa."

Ta kara da cewa an damke mahaifiyar barawon, Mrs Tale Akinlabi, saboda ita ke ajiye masa kayan sata.

Kakakin yan sandan tace nan ba da dadewa ba za a gurfanar da su kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: