Wani mutumi ya fara tattaki daga Bauchi zuwa Legas don Asiwaju Bola Tinubu

Wani mutumi ya fara tattaki daga Bauchi zuwa Legas don Asiwaju Bola Tinubu

  • Dan jihar Bauchi mai tattaki daga Bauchi zuwa Legas don Tinubu ya dira garin Ilori ranar Talata
  • Madaki yace shi dan a mutum Tinubu ne kuma yana son haduwa da shi a Legas don taya shi murnar nasara a zabe
  • Asiwaju Bola Tinubu ne dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyya mai mulki ta APC

Wani dan shekara 51, Usman Madaki, yana kan tattaki daga jihar Bauchi zuwa jihar Legas don taya dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, Ahmed Bola Tinubu, murna.

Mutumin ya isa garin Ilori daren Talata kuma ya tashi ranar Laraba ya nufi Ibadan, rahoton DailyNigerian.

Ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN cewa duk da cewa bai taba haduwa da Tinubu a rayuwarsa ba, shi babban masoyin Bola Tinubu ne.

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

Madaki
Wani mutumi ya fara tattaki daga Bauchi zuwa Legas don Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Malam Madaki dan asalin garin Bauchi ya fara tattakin ne ranar 10 ga Yuni kuma yana da niyyar dira Legas ranar Asabar, 25 ga Yuni, 2022.

Yace:

"Ina son haduwa da Tinubu a Legas don taya sa murna bisa nasarar da yayi na zama dan takarar kujerar shugaban kasa na APC."
"Ina da imanin cewa shi zai zama shugaban kasa gobe. Ina son Tinubu, mai gidana ne duk da cewa bai san ni ba."
"Zan tafi jihar Oyo yau, ina ganin babu nisa."

Madaki ya bayyana cewa yana neman jigon APC da zai hada shi da Tinubu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel