Allah wadaran naka ya lalace: Yadda wata Ma’aikaciyar lafiya ke siyar da Jarirai N250,000
- ‘Yan sanda sun cafke wata Ungozoma mai suna Regina Ibeto a garin Legas bisa laifin siyar da Jarirai ‘yan sati guda kan kudi Naira N250,000
- Amma sai dai ita ta ce idan ba'a yaba mata ba to tabbas bai kamata a zage ta ba, domin taimako tayi
An dai yi holar Matar ne a jiya tare da Kwastomominta Udoju Chukwunoye da Joy James, tun bayan da aka kama Ma’aikaciyar lafiyar mai shekaru 50 ne a ranar 23 ga watan Mayu a gidanta dake lamba 96, kan Titin Bunmi Ajakaye dake unguwar Ajangbadi.
A cewar ‘yan sandan, Ibeto ta kasance kwararriyar mayaudariyar Mata masu ciki ce wadda da zarar sun haihu sai ta lababa ta yaudare su sannan ta siyar da jaririn.
Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar ta Legas Imohimi Edgal ya ce, bayan da suka samu labarin irin wannan aika-aikar da take aikatawa ne, sai suka kaimata farmaki suka kuma yi nasarar damko ta har kuma a lokacin suka tarar da ita tana karawa wata mai shirin haihuwar ruwa mai suna Uju Nnamdi.
KU KARANTA: Ranar Yara ta Duniya: Daga yanzu duk mai abin hawan da ya kade yara zai shekara 2 a kurkuku
Sai bayan da taji matsa a hannun ‘Yan sanda, Ibeto ta zayyana cewa dama ita ba Ma’aikaciyar lafiya ba ce, kawai dai ita ta kasance tana karbar haihuwa ne a gargajiyance.
A ranar 18 ga watan Mayu ne Ibe ta yaudari wata Mata mai suna Bukky ‘yar shekara 17 da cewa ita Ma’aikaciyar lafiya ce, inda bayan ta haihu suka siyarwa Udoju Chukwunoye jaririn kan kudi N250, 000. Amma sai dai an samu nasarar kama shi aka kwato jaririn sannan aka kai shi Asibiti don duba lafiyarsa.
Yayinda aka kuma kaddamar da bincike kan Mahaifiyar Jaririn, sai dai ita Ibeto ta ce Mahaifiyar Jaririn Bukky ce ta ce bata son Dan nata kasancewar cikin shege ne.
“Bayan da Bukky ta bayyana min irin halin takura da Mahaifinta ya sanya ta ne na tausaya mata domin tayi kankanta ta haifi Dan cikin shege, shi ne na tausaya mata na kira wadda zata siyi Jaririn nata, na kuma bata wani kaso daga cikin kudin domin ta fara sabuwar rayuwa sanann na shawarce ta tayi hattara.”
"Ni ban aikata laifin komai ba domin taimakon Yarinyar nayi a loakcin da take cikin mawuyacin hali, amma sai ga ‘Yan sanda sun shigo cikin gida na sun kama ni da laifin yaudarar Mata sannan bayan sun haihu ina siyar da ‘ya’yan nasu."
Sanna 'yan sandan kuma suka ce tayin sojan gona da cewa ita Ma’aikaciyar Lafiya ce, wanda ita kuma ta ce ba haka ba ne kasancewar bata taba fadar haka don ita Ungozoma ce ta gargajiya. A cewar Ibeto.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng