APC ta nada Ganduje shugaban yakin neman zaben Gwamnan jihar Osun
- Jam'iyyar APC ta zabi mutum 81 da zasu taya ta yakin neman zaben gwamnan jihar Osun a watan Yuli
- Gwamnan jihar Kano aka baiwa hakkin tabbatar da APC ta lashe zaben jihar Osun da zai gudana watan gobe
- Gwamna Gboyega Oyetola na neman zarcewa kan kujerar mulki bayan shekaru hudu na farko
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta sanar da mambobin kwamiti mutum 81 da zasu yiwa jam'iyyar yakin neman zaben gwamnan jihar Osun.
Hukumar INEC zata gudanar da zaben gwamnan jihar ne ranar 16 ga Yuli, 2022.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan Legas Babajide Sanwoolu, aka nada su jagoranci kwamitin.
A jerin sunayen da shugaban uwar jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu, ya fitar ranar Talata, yace an baiwa wannan kwamiti hakkin tabbatar da cewa dan takarar jam'iyyar, Gboyega Oyetola, ya lashe zaben.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
Za'a rantsar da kwamitin ranar Alhamis a sakatariyar jam'iyyar dake Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Asali: Legit.ng