Gwamna Matawalle ya ceto mutane 3,000 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Zamfara

Gwamna Matawalle ya ceto mutane 3,000 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Zamfara

  • Gwamnatin jihar Zamfara karƙashin Bello Matawalle ta bayyana ɗumbin nasarorin da ta samu a ɓangaren tsaro tun farkon zuwanta
  • Kwamishinan labarai, Ibrahim Dosara, ya ce daga 2019 zuwa yau gwamnati ta kubutar da dubbannin mutane daga hannun masu garkuwa
  • Ya ce sabon shirin da gwamna Matawalle ya zo da shi na tattaunawar sulhu da yan bindiga ya haifar da sakamako mai kyau

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara karakashin gwamna Bello Matawalle ta bayyana cewa ta yi nasarar kuɓutar da mutane 3,000 daga hannun masu garkuwa daga 2019 zuwa yau.

Kwamishinan labarai, Ibrahim Dosara, ne ya faɗi haka a Gusau ranar Talata yayin da yake tsokaci kan nasarorin da ayyukan tsaro suka haifar a faɗin jihar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Bello Matawalle na Zamfara.
Gwamna Matawalle ya ceto mutane 3,000 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Zamfara Hoto: Ibrahim Bello Zauma/facebook
Asali: Facebook

Ya ce mutanen sun kuɓuta ne ta hanyar shirin zaman lafiya, sulhu da tattaunawa wanda gwamnatin gwamna Muhammad Bello Matawalle ta kirkiro a shekaru uku da suka shude.

Kara karanta wannan

An gano gawar wata mata cikin yanayi a Abuja, wasu abu biyu na kusa da ita sun ɗaga hankulan mutane

A jawabinsa kwamishinan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kafin zuwan gwamnatin Matawalle, jihar Zamfara ta tsinci kanta cikin mummunan hali na rashin tsaro, musamman yawan kai hare-hare kauyuka da kuma garkuwa da mutane."
"Bayan ya ƙarbi mulki a matsayin gwamna, Matawalle ya ƙirƙiro shirin tattaunawa da sulhu tsakanin gwamnati da ƴan bindiga. Shirin tattaunawan ya haifar da ɗa mai ido sabida Zaman lafiya ya fara dawowa jihar mu."

A cewar Dosara, ayyukan yan bindiga ya ragu matuƙa a dukkan sassan jihar Zamfara, inda ya kara da cewa sai da aka shafe watanni Tara ba'a kai hari ba a farkon shirin zaman lafiyan.

Yadda Gwamnatin Matawalle ta kuɓutar da mutane

Kwamishinan ya ce gwamnati ta yi nasarar kubutar da tawaga daban-daban ta mutanen da maharan suka yi garkuwa da su, waɗan da suka haɗa da maza, mata da kananan yara, wasu sun fito ne daga Katsina da Sokoto.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun yi farin ciki, an tsinci gawawwakin ‘yan ta’adda jibge a cikin rafi

Dosara ya ce adadi mai yawa na ƴan bindiga sun mika wuya ga hukumomin tsaro yayin da aka lalata sansanonin su da dama tun farkon zuwa shirin tattaunawar zaman lafiya.

Bugu da ƙari ya ce hanyoyin da aka rufe saboda matsalar yan bindiga yanzun an buɗe su don mutane su cigaba da harkokinsu, a cewarsa kananan hukumomi 14 na jihar ba su da matsalar tsaro a hanya.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar babban jigon APC ɗan takara a 2023

Myagun yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun sace mahaifiyar ɗan takarar Sanatan Jigawa ta tsakiya a garin Kiyawa.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Shisu, ya ce tuni kwamishina ya haɗa tawagar dakaru na musamman don ceto matar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262