Wike ya cika surutu, shi yasa Atiku yaki daukansa: Tsohon gwamna Babangida Aliyu

Wike ya cika surutu, shi yasa Atiku yaki daukansa: Tsohon gwamna Babangida Aliyu

  • Babangida Aliyu ya bayyana dalilin da yasa Atiku yaki zaben gwamnan Rivers matsayin mataimakinsa
  • Tsohon gwamnan Nejan yace surutun Wike ya yi yawa kuma zai iya zama wa Atiku matsala gobe
  • Babangida yace Wike ya shahara da zagin mutane da dama kuma ba kowa ke jin dadin harka da shi ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon gwamnan jihar Neja kuma jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Babangida Aliyu, ya bayyana daya daga cikin dalilan da yasa aka ki zaben gwamnan RIvers, Nyesom Wike, matsayin abokin tafiyar Atiku Abubakar.

A cewar Aliyu, Nyesom Wike ya fiye surutu shi yasa ba'a zabesa ba.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a hirarsa da ChannelsTV.

Yace:

"Ba zai yiwu ka zabi mutumin da ba zai kara maka komai ba. A matsayinka na shugaba, za ka zabi mutumin da zai zama mai amfani da ofishinka."

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

"Ban sani ba ko yawan fushi ne ko wani abun, idan mutum ya fiye surutu, ko ya rika zagin mutane . Akwai mutane da dama da na sani basu jin dadin kalaman da yake yi da sunan fadin ra'ayinsa. Akwai lokutan da ba komai mutum ke fadi ba."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

wike Atiku
Wike ya cika surutu, shi yasa Atiku yaki daukansa: Babangida Aliyu
Asali: Twitter

Zaben 2023: Magoya bayan Wike sun fara barazana a kan dauko Okowa

Wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP na jihar Ribas sun soki zabin da Alhaji Atiku Abubakar ya yi na dauko Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takaransa.

Legit.ng ta samu labari cewa wadannan masu ruwa na jam’iyyar hamayyar sun fito su na zargin Atiku Abubakar da kin girmama abin da PDP ta yanke.

Shugaban karamar hukumar Ikwerre a jihar Ribas, Dr. Samuel Nwanosike ya ja-kunnen ‘dan takaran da cewa zai ga tasirin wannan danyen zabi na sa.

Kara karanta wannan

An samu mummunan yamutsi a PDP, rikici ya ki karewa a kan abokin takarar Atiku Abubakar

Dr. Nwanosike yake cewa Atiku Abubakar bai girmama jam’iyya ba saboda ya ki daukar zabin kwamiti na musamman da aka kafa domin wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: