Hankula sun tashi: An gano gawar wata mata cikin wani yanayi a Abuja

Hankula sun tashi: An gano gawar wata mata cikin wani yanayi a Abuja

  • Mutanen garin Kubwa a babbar birnin tarayya Abuja sun wayi gari ranar Litinin cikin tashin hankali
  • Bayanai sun nuna cewa mazauna ƙaramin garin sun gano gawar wata mata a juji tare da gawarwaki biyu a kusa da ita cikin wani yanayi
  • Hukumar yan sanda ta FCT Abuja ta ce ta fara bincike don gano amsoshin tambayoyin da suka baibaye lamarin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Mazauna Kubwa, wani gari da ke karƙashin babban birnin tarayya Abuja sun shiga yanayin kaɗuwa ranar Litinin biyo bayan abun da suka gano a wata Bola.

Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen garin sun tsinci gawar wata mata da aka daddatsa tare da gwarwakin wasu dabbobi biyu kusa da ita a bayan gadar PW, lamarin da ya tayar musu da hankali.

Kara karanta wannan

Karfin hali: ‘Yan sanda sun cafke wasu mutane 6 da ake zargin ‘yan fashin banki ne

Wurin da aka tsinci gawar wata mata a Abuja
Hankula sun tashi: An gano gawar wata mata cikin wani yanayi a Abuja Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Gawar dabbobin, Akuya da kuma Kare a cikin buhuna daban-daban an tsince su a bayan gawar matar, wacce aka raba sassan jikin ta zuwa gida Tara.

Bayanai sun nuna cewa kowane sashi na jikin matar na nan yadda yake amma ban da gaɓar hannun ta, shi ne ake ganin an cire.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Wani mai gadi da ke aiki a ɗaya daga cikin wuraren kasuwancin mutane kusa da wurin da abun ya faru, ya ce sun wayi gari ne suka ga gawar matar wacce aka yi gunduwa gunduwa da ita.

Shugaban caji Ofis ɗin Kubwa, DPO, CSP Abubakar Abdulkarim, ya tabbatar da lamarin mai ɗaure kai da ake zargin yana da alaƙa da yan ƙungiyar Asiri.

Jami'in hukumar yan sandan ƙasar nan ya ce a halin yanzun sun fara gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar matar ta wannan halin.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun yi farin ciki, an tsinci gawawwakin ‘yan ta’adda jibge a cikin rafi

Da yake tabbatar da lamarin a rahoton Punch, Kakakin yan sandan FCT Abuja, Omotayo Oduniyi, ya ce:

"A yanzun ba zamu tabbatar da zargin wasu mutane da ke ganin lamarin ya shafi yan asiri ba, mun fara bincike don gano amsoshin duk wasu tambayoyi."

A wani labarin kuma Kotu ta yanke wa Miji hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda ya kashe kwarton matarsa

Kotu ta ba da umarnin a rataye wani Magadinci har Lahira bayan kama shi da laifin kashe wani da yake zargin yana wa matarsa kwartanci.

Da take yanke hukunci, Mai Shari'a Patricia Oduniyi, ta ce Hujjojin da aka gabatar mata sun tabbatar ta laifin wanda ake zargi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: