Kotu ta yanke wa wani Magidanci hukuncin kisa saboda ya kashe kwarton matarsa
- Kotu ta ba da umarnin a rataye wani Magadinci har Lahira bayan kama shi da laifin kashe wani da yake zargin yana wa matarsa kwartanci
- Da take yanke hukunci, Mai Shari'a Patricia Oduniyi, ta ce Hujjojin da aka gabatar mata sun tabbatar ta laifin wanda ake zargi
- Lauya mai shigar da ƙara ya shaida wa Kotu tun farko yadda wanda ake ƙara ya sa bindiga ya kashe mamacin a gona
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Ogun - A ranar Litinin Babbar Kotun Aiyetoro da ke jihar Ogun ta yanke wa wani mutumi mai suna, Adelake Bara, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa harbe wani, Olaleye Oke, har Lahira.
Premium Times ta ruwaito cewa Magidanci ya harbe mutumin ne bisa zarginsa da cin amana da ƙulla ɓoyayyar alaƙa da ɗaya daga cikin matansa guda uku.
Kotun ta kama Mista Bara da laifi ɗaya wanda tun farko aka gurfanar da shi kansa wato kisan kai.
Da take bayyana hukuncin Kotu a zaman yau, Alkalin Kotun mai shari'a Patricia Oduniyi, ta ce ɓangaren masu shigar da ƙara sun gamsar da Kotu da hujjoji da suka zarce tantama kansu kan cewa wanda ake zargi shi ya aikata kisan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Misis Oduniyi ta ce laifin da mutumin ya aikata ya saɓa wa kundin dokoki manyan laifuka 'Criminal Cide' na jihar Ogun.
Yadda zaman Kotu kan lamarin ya gudana
Yayin zaman sauraron ƙarar, Lauyan jiha mai shigar da ƙara, T.O Adeyemi, ta faɗa wa Kotu cewa mutumin da ake zargin ya aikata laifin a ranar 1 ga watan Mayu, 2022 da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.
Mis Adeyemi, ta ƙara da cewa Mamacin na gona lokacin da Mista Bara ya same shi, ya fara caɓa masa maganganun zargin yana neman ɗaya daga cikin matansa.
Tsautsayi: Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook
Ya ce:
"Mista Bara wanda ke da mata har uku, ya zaro bindiga ya harbi mista Oke a tsakiyar kai yayin da yake kokarin yi masa bayanin cewa zargin da yake masa ba gaskiya bane."
Lauyan ya ƙarƙare da cewa wannan harbin ya yi wa Oke, shi ne sanadin mutuwarsa, kamar yadda PM News ta ruwaito.
A wani labarin na daban kuma 'Yan sanda sun yi kazamin artabu da 'yan bindiga a jihar Zamfara, rai ya salwanta
Dakarun hukumar yan sanda a jihar Zamfara sun yi nasarar halaka ɗan bindiga ɗaya a wata musayar wuta ta tsawon awanni.
Kakakin yan sandan jihar, Muhammed Shehu, ya ce jami'an da haɗin guiwar yan bijilanti sun daƙile yunkurin kai hari wasu ƙauyuka biyu.
Asali: Legit.ng