Da dumi-dumi: Tsohon gwamnan Ribas da Filato na mulkin soja, Kanal Shehu, ya rasu
- Tsohon gwamnan Ribas da Filato na mulkin soja, Kanal Musa Sheikh Shehu mai ritaya, ya kwanta dama.
- Marigayin wanda ya rike mukamin gwamnan karkashin mulkin Janar Sani Abacha ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni.
- Tuni aka yi jana'izarsa a makabartar Gudu da ke babbar birnin tarayya Abuja bayan an yi masa sallah a unguwar Apo
Abuja - Rahotanni sun kawo cewa wani tsohon gwamna a mulkin soja, Kanal Musa Sheikh Shehu mai ritaya ya rasu.
Wata majiya ta kusa da iyalan ta bayyana cewa Kanal Shehu ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni, PR Nigeria ta rahoto.
Majiyar ta ce za a binne marigayin wanda ya kasance gwamnan jihar Filato na mulkin soja da misalin karfe 1:30 na rana a makabartar Gudu bayan an yi masa sallah a unguwar Apo.
Marigayin ya kasance dan asalin jahar Sokoto ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kasance gwamnan soja na jihar Ribas daga Agustan 1996 zuwa Agustan 1998 a karkashin mulkin Janar Sani Abacha, sannan ya koma gwamnan soja na jihar Filato har zuwa lokacin da mulkin damokradiyya ya dawo a watan Maris 1999.
A 2010, Shehu ya kasance babban sakataren kungiyar tuntuba ta arewa (ACF), Solacebase ta rahoto.
Yan bindiga sun sake kai hari Jihar Bauchi, sun sace Basarake da ɗansa
A wani labari na daban, mun ji cewa yan bindiga su farmaki ƙauyen Zira da ke ƙaramar hukumar Toro, jihar Bauchi, inda suka yi awon gaba da Dagacin garin, Yahaya Saleh Abubakar, da ɗansa, Habibu Saleh.
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a ruwayar Daily Trust.
Ya ce ƴan bindigan sun shiga ƙauyen wanda ke ƙarƙashin Caji Ofis ɗin Rsihi kuma mai iyaka da jihar Filato, da misalin ƙarfe 2:00 na daren ranar Asabar.
Asali: Legit.ng