Manyan gobe: Hotunan yaro mai burin zama sojan ruwa sun bar jama'a baki bude
- Wani yaro ya zo makaranta a ranar burin aiki sanye da kaya kamar jami'in sojan ruwa, lamarin da ya ba da mamaki
- Mahaifiyar yaron cikin alfahari ta saka hotuna guda biyu na yaron lokacin da aka dauke shi a makaranta a cikin kakin sojan ruwa a shafin Twitter
- Jama'a a Twitter da suka ga hotunan sun ka da baki sun yi martani, inda suka bayyana yadda suka ji game da yaron
Wani karamin yaro ya burge kowa da kwalliyarsa mai ban mamaki yayin da ya fito a ranar burin aiki ta makarantarsu sanye da kakin jami’in sojan ruwa, hotunan sun yadu a duniya.
Mahaifiyar yaron, wacce aka fi sani da @chefbanke a shafin Twitter, ta bayyana kyawawan hotunan yaron nata da ke sanye da kakin sojin ruwa, sannan ta bayyana alfahari dashi.
Bidiyo: Dan Majalisar Tarayyar Najeriya Ya Bada Umurni An Nuna Alat Din Albashinsa Na Watan Mayu a Talabijin
Da take yada hotunan a shafinta na Twitter, ta ce:
"Ranar burin aiki a makarantar su dan da na, kuma ya bayyana kamar haka."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jama'a da dama da suka yi na'am da ganin hotunan, sun kuma nuna sha'awarsu da bayyana alfahrinsu gareshi.
Ya zuwa lokacin hada rahoton nan, rubutu da hotunan sun samu martani sama da 6000 a dangwale 61.8K.
Martanin jama'ar Twitter
@Nharkita yace:
"OMG. Wannan ya sha kyau.''
@nayaliving:
''Wannan ya sha kyau sosai.''
@Oladele89407315 ya ce:
''Ina son wannan!''
@michael_spiff ya ce:
''Ina so in san nawa ne kudin takalman nan.''
@_OnahGrace ya ce:
''Wannan shiga ta yaro."
@adesolaaaa ya yi sharhi dacewa:
''Abin ban sha'awa! Ina son wannan sutura!''
A kama sana'a: Mata ta kammala digiri da 1st class, ta ba da mamaki da fara sana'ar kitso
A wani labarin, duk da cewa Theresah Adusei ta kammala karatun digiri da sakamakon '1st class' fannin ilimin bayanai da halayyar dan adam a Jami'ar Ghana, ta sha fama domin ganin ta samu aiki.
A 2019, ta sanya kanta da danginta alfahari a lokacin da ta kammala jami’a da lambar yabon karramawa, amma a yanzu burinta na samun kyakkyawan aiki ya zama tamfar yasan teku da moda.
A wata hira da tayi da Joy Prime, Adusei ta bayyana cewa ta fara fafutukar neman aikin ta ne a lokacin da ta kusa kammala hidimar kasa.
Asali: Legit.ng