Da duminsa: Peter Obi ya zabi Kirista, dan Kudu matsayin mataimakinsa
1 - tsawon mintuna
- Mai nema zama shugaban kasa a 2023 karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi, ya zabi Doyin Okupe matsayin abokin tafiyarsa
- Peter Obi, wanda yayi murabus daga PDP ana jajibirin zaben fidda gwani ne jam'iyyar Labour Party ta tsayar
- Doyin Okupe ya kasance na hannun daman tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Doyin Okupe, a ranar Juma'a ya bayyana cewa shine aka zaba matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi.
Doyin Okupe ya bayyana hakan a hirarsa da Seun Okinbaloye na tashar ChannelsTV.
Peter Obi ya bi sahun Tinubu wajen zaben mai addini daya da shi matsayin abokin tafiya.
Amma ana hasashen cewa an sanya sunan Okupe ne kawai don kada wa'adin INEC ta cika, daga baya akwai yiwuwa a sauya sunansa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Asali: Legit.ng