Za'a yiwa Gwamna Ganduje da Gwaggo nadin sarauta a garin Ibadan

Za'a yiwa Gwamna Ganduje da Gwaggo nadin sarauta a garin Ibadan

  • Mai Martaba Olubadan of Ibadan zai yiwa gwamnan jihar Kano da Uwargidarsa nadin sarauta
  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai zama Aare Fiwajoye na kasar Ibadan kuma Gwaggo Yeye Aare Fiwajoye
  • Masarautar Ibadan tace wannan nadin sarautan zai kara dankon zumunci tsakanin Yarabawa da Kano

Za'a yiwa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, nadin sarautan 'Aare Fiwajoye' na garin Ibadan yayinda za'a yiwa uwargidarsa, Hajiya Hafsat, nadin Yeye Aare Fiwajoye.

Sarki (Olubadan) na garin Ibadan ne zai yiwa gwamnan nadin ranar Asabar, 18 ga watan Yuni, 2022, rahoton TheNation.

Mai magana da yawun Sarkin Ibadan, Oladele Ogunsola, ya bayyana cewa za'a yiwa Ganduje nadin ne bisa shawarar Sarkin Yarbawa mazauna jihar Kano, Alhaji Murtala Alimi Otisese (Adetimirin-1).

Yace:

"Wannan nadi zai kara karfin alaka tsakanin kasar Ibadan da al'ummar Kano."

Kara karanta wannan

Adadin yaran da basu zuwa makaranta a Najeriya ya kai milyan 18, Gidauniyar McArthur

Ganduje, a jawabin amsa wannan gayyata da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kano, Usman Muhammad, yayi, ya bayyana cewa wannan nadi zai kara dankon zumuncin dake tsakanin Oyo da Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gandujes
Za'a yiwa Gwamna Ganduje da Gwaggo nadin sarauta a garin Ibadan Hoto: African House
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel