Cikakken Jerin sunayen kwamandojin ISWAP da Sojojin Najeriya suka tura Lahira

Cikakken Jerin sunayen kwamandojin ISWAP da Sojojin Najeriya suka tura Lahira

Ƙungiyar ta'addanci ISIS ta fitar da cikakken jerin kwamandojin mayaƙan ISWAP da gwarazan sojoji suka samu nasarar tura su barzahu su haɗu da Allah.

Sojojin Najeriya tare da haɗin guiwar rundunar sojin ƙasa da ƙasa sun ragargaji yan ta'addan a wani gumurzu da suka yi makonni kalilan da suƙa shuɗe.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Dakarun Soji suka kaddamar da manyan hare-hare kan mayaƙan ISWAP a yankin Tafkin Chadi da kuma dajin Sambisa.

Sojojin Najeriya.
Cikakken Jerin sunayen kwamandojin ISWAP da Sojojin Najeriya suka tura Lahira Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Sojojin sun farmaki sansanin yan ta'addan, wanda ke tattare da mayaƙa kusan 3,000 da ke goyon bayan tsagin Abubakar Sheƙau na Boko Haram.

Mayaƙan Boko Haram ɗin sun koma tsagin ISWAP, bayan ƙungiyar ta halaka shugaban su Abubakar Shekau a shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Borno: Hotunan Tubabbun 'Yan Boko Haram 204 Yayin da Suka Mika Kansu ga Sojoji

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani rahoton fasaha, Sojojin da kuma yan ta'addan sun gwabza a wata doguwar musayar wuta da ta shafe sama da awanni uku ana artabu.

Bayan wannan dogon artabu, dakarun soji sun samu nasarar kama kwamandojin yan ta'addan guda biyu, yayin da wasu da dama suka bakunci lahira.

A wani bidiyo da ISIS ta fitar, ta bayyana sunayen kwamandojin ISWAP da suka rasa rayukansu a hannun sojoji.

Ga su kamar haka:

1. Abu Musab al-Yobawi

2. Abu Nu’man al-Amni

3. Abu Abdullah al-Barnawi

4. Abu ‘Ammara al-Barnawi

5. Abu Anas al-I’alami

6. Abdul Malik al-Barnawi

7. Abu Sufyan al-I’alami

8. Shaykh Abu Bakr al-Da’wi

9. Abu Usama Goneri

10. Abu Sa’d al-Ansari

11. Abu Jabbar al-Barnawi

12. Abu Anas al-Barnawi

13. Abu Abdul Rahman al-Katsanawi

14. Abu Maryam al-Gaidami

15. Abu Salman al-Ansari

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Shin APC ta yi wa Kiristocin Arewa adalci? daga Muhammad Auwal

16. Baka Goneiri

17. Abu Mustafa al-‘Askari

18. Farooq al-Barnawi

19. Abu Ahmad al-I’alami

20. Al-Qassim Al-Barnawi

21. Mustafa al-Barnawi

22. Abbas al-Ansari

23. Musa al-Ansari

Labarin kashe kwamandojin na zuwa ne kawanaki kaɗan bayan an zargi ƙungiyar da kai hari wata Coci a Owo jihar Ondo, wanda ya yi sanadin mutuwar masu ibada da dama.

A wani labarin na daban kuma Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook

Kotu ta ɗaure wani mutumi na tsawon wata biyu a gidan Gayaran hali bayan kama shi da laifin yaɗa ƙarya kan COVID19 a Facebook.

Mutumin mai suna, Habibu Rabiu, ya yi wani rubuta inda ya ankarar da mutane cewa rasa rayuka na ƙaruwa a Kogi sanadiyyar zazzaɓi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: