Yanzu-yanzu: Musulmai sun yi nasara, kotun koli tayi watsi da dokar hana sanya Hijabi a makarantun Legas
- Iyayen dalibai Musulmai sun yi nasara, kotun koli tayi watsi da dokar hana sanya Hijabi a makarantun Legas
- Kotun kolin Najeriya ta kawo karshen dambarwan bayan shekaru takwas ana kai ruwa rana
- Irin wannan lamari na Hijabi yanzu haka na gudana a jihar Kwara inda wasu makarantu suka hana dalibai sa Hijabi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Kotun koli ta baiwa Musulmai gaskiya inda tayi watsi da karar da gwamnatin jihar ta shigar kan hana dalibai mata Musulmai sanya Hijabi a makaratun dake fadin jihar.
A hukuncin da kotun ta yanke ranar Juma'a, 17 ga watan Yuni, 2022, ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara tayi ranar 21 ga Yuli, 2016.
Cikin alkalan kotun koli bakwai da suka zauna kan lamarin, biyar sun amince a bari daliban su sanya Hijabansu yayinda biyu suka ce basu yarda ba, rahoton TheNation.
Bai Tsinana Mana Komai Ba: Matasa Da Mata Sun Huro Wuta A Karamar Hukuma, Sun Ce Dole A Tsige Ciyaman
Alkali Kudirat Kekere-Ekun, wacce ta rubuta shari'ar da Alkali Tijjani Abubakar, ya karanto ranar Juma'a, tace ayi watsi da karar gwamnatin Legas saboda babu gaskiya ciki.
Zaku tuna cewa kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin kotun jihar Legas na ranar 17 ga Oktoba, 2014 da Alkali Grace Onyeabo na Legas ta yanke cewa a hana dalibai sanya Hijabi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Asali: Legit.ng