Borno: Hotunan Tubabbun 'Yan Boko Haram 204 Yayin da Suka Mika Kansu ga Sojoji

Borno: Hotunan Tubabbun 'Yan Boko Haram 204 Yayin da Suka Mika Kansu ga Sojoji

  • Tubabbun mayakan ta'addanci na Boko Haram har su 204 ne suka mika wuya ga rundunar sojin Najeriya dake Borno
  • Lamarin ya faru a ranar Laraba, 15 ga watan Yuni yayin da suka garzaya tare da iyalansu har garin Bama domin tuba
  • Kamar yadda hedkwatar rundunar sojin kasan Najeriya ta sanar tare da bayyana hotuna, ana daukan bayanansu daya bayan daya

Borno - Sakamakon tsananta ragargaza da ruwan wuta da rundunar sojin Najeriya ke yi wa 'yan ta'adda domin kawo karshen ta'addanci, ana ta samun manyan nasarori masu yawa.

Kamar yadda hedkwatar rundunar sojin kasa ta najeriya ta bayyana, ana samun nasara wacce aka kara samu a ranar 15 ga watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji da CJTF sun halaka dandanzon yan ta'adda, sun lalata kasuwa da sansanin su a Borno

mayakan ta'adanci na Boko Haram har su 204 ne suka yadda makamai tare da mika wuya ga sojojin Najeriya.

'Yan ta'addan tare da iyalansu sun garzaya har karamar hukumar bama ta jihar Borno inda suka mika wuya ga sojojin Najeriya.

Hoton Tubabbun 'Yan Ta'addan Boko Haram Yayin Da Suka Mika Wuya ga Sojin Najeriya
Borno: Hotunan Tubabbun 'Yan Boko Haram 204 Yayin da Suka Mika Kansu ga Sojoji. Hoto daga @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, ana daukan bayanan tubabbun 'yan ta'addan a halin yanzu.

Kano: Yadda 'Dan Ta'addan ISWAP ya Samu Gidan Zama, Ya Siya Filaye 5 da Taimakon Jami'in Hisbah

A wani labari na daban, a cikin kwanakin nan ne jami'an tsaro suka yi ram da wani 'dan ta'addan ISWAP a jihar Kano. Ya hada alaka da jami'in hukumar Hisbah a jihar wanda ya taimaka masa ya siya filaye kuma ya kama gidan haya.

'Dan ta'addan mai sunaye da yawa kamar Malam Abba da Adamu Makeri, ya hadu da jami'in hukumar Hisbah a wani darasin Larabci da yake halarta a Masallacin Almuntada, Masallacin 'yan salaf dake Dorayi a jihar Kano kamar yadda bayanan jami'an tsaro suka bayyana.

Kara karanta wannan

Hari Da Taimakon Jirgin Sama: Mazauna Kajuru Sun Bayyana Tashin Hankalin da Suka shiga

HumAngle ta ruwaito cewa, alakar ta bai wa 'dan ta'addan damar kama haya a yankin Samegu dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano na sama da shekaru hudu kafin dubunsa ta cika a farkon watan Yuni.

Wurin yana da kusanci da inda jami'an tsaro na farin kaya suka kama wata mota dankare da makamai.

Bayanin ya bayyana cewa, 'dan ta'addan ya roki jami'in Hisban da yayi amfani da isar sa wurin sama masa haya bayan bayyana masa da yayi yana kwana a wata ma'ajiyar kayayyaki ne. Daga bisani ya sanar da jami'in cewa zai kwaso iyalansa daga jamhuriyar Nijar kuma yana neman taimakonsa wurin samun wani gidan haya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: