Lai: FG Ta Matukar Damuwa Da Yajin Aikin ASUU, Muna Aiki Kan Shawo Kan Shi

Lai: FG Ta Matukar Damuwa Da Yajin Aikin ASUU, Muna Aiki Kan Shawo Kan Shi

  • Gwamanatin tarayya ta bayyana yadda ta shiga damuwa game da cigaba da yajin aikin kungiyar malamai masu koyarwa na jami'a (ASUU)
  • Ministan yada labarai, Lai Muhammad, ya kara da cewa lamarin ASUU ba abu bane mai sauki kamar yadda wasu suke gani
  • Haka zalika, ya ce duk da matsalar ASUU da ke gaban gwamnatin, ba za tayi kasa a guiwa wajen bunkasa ilimin firamere ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar 14 ga watan Fabrairu, ASUU ta tafi yajin aikin wata daya don nuna rashin amincewarta bisa bukatunta da gwamnati ta gaza cikawa.

A ranar 14 ga watan Maris, kungiyar ta kara makwanni takwas a kan yajin aikin, saboda yadda gwamnati ta gaza biya mata bukatunta, The Cable ta ruwaito.

Kungiyar Daliban Najeriya NANS, Yayin Da Suka Fito Zanga-Zanga
Lai: FG Ta Matukar Damuwa Da Yajin Aikin ASUU, Muna Aiki Kan Shawo Kan Shi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Daga bisani, kungiyar ta sake kara wasu makwanni 12 a kai.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kamfanonin Jiragen Sama a Najeriya Za Su Tsayar Da Aiki Saboda Tsadar Man Jirgin Sama

Baya ga ASUU, kungiyar manyan malaman jami'oin Najeriya (SSANU), kungiyar malamai marasa koyarwa na jami'oi da sauran makarantun gaba da sakandiri (NASU), tare da kungiyar masu ilimin fasaha ta kasa (NAAT) duk sun dakata da aiki saboda irin yadda "Gwamnati ta nuna halin ko in kula" ga bukatunsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Channels TV ta ruwaito cewa, yayin zantawa a ranar Laraba bayan fitowa daga taron majalisar zartarwar tarayya (FEC), Lai Muhammad, ministan yada labarai da al'adu, ya ce lamarin kungiyar ba abu bane mai sauki kamar yadda ake tunani.

"Ba na tunanin saboda muna fuskantar kalubale daga malamai masu koyarwa a jami'a, kawai sai mu tsaida daliban firamare daga cigaba da karatu," a cewarsa.
"Sannan na so a ce lamarin ASUU na da sauki kamar yadda da yawanmu ke tunani. Ba na ganin yana da saukin nan. Amma ina so in tabbatar muku da cewa akwai wani abu da ke faruwa a bayan fage.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

"Ina tunanin ta yuwu ministan ilimi shi ne zai iya bada cikakken bayani. Amma kamar kowacce gwamnati, da a ce ba mu damu ba, ba za mu shirya kwamitin da ke aiki a kan lamarin ba.
"Da a ce ba mu damu ba, ba za mu nemi yadda za mu shawo kan kungiyar ba.
"Mun shiga damuwa. Mun kuma damu, sannan za mu cigaba da aiki wajen ganin mun shawo kan matsalar da wuri."

Ya kara da cewa, gwamanatin tarayya ta amince da bude cibiyoyin na'ura mai kwakwala ga daliban firamere na fadin kasar nan.

Majalisar zartarwa ta ASUU na tattaunawa, ta yuwu a kara wa'adin yajin aiki

A wani labari na daban, mambobin majalisar zartarwa ta Kungiyar Malamai masu Koyarwa ta Jami'o'in Najeriya a halin yanzu sun shiga ganawa, jaridar Punch ta gano hakan.

Wani mamban majalisar zartarwar ya sanarwa da Punch cewa ta yuwu a kara wa'adin yajin aikin duba da abinda ake tattaunawa a cikin taron yanzu.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Yan Najeriya basu damu da addinin yan takara ba – Baba Ahmed

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng