Da dumi-dumi: Sojoji sun gano wata mata da Boko Haram suka sace tun 2014
- Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa, ta gano wata mata da ke garari a wani yankin Borno, wacce 'yan Boko Haram suka sace
- Rahoton soji ya ce ana kyautata zaton matar na daga cikin 'yan matan Chibok da aka sace a shekarar 2014
- Hakazalika, an gano ta ne tare da yaro, kana ana ci gaba da bincike don gano asalin tsuhen batan ta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Borno - Dakarun runduna ta 26 Task Force Brigade, a ranar Talata, sun gano wata Mary Ngoshe, wacce a cewar rundunar sojin Najeriya, tana daya daga cikin ‘yan matan da aka yi garkuwa da su a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke Chibok a shekarar 2014.
Ngoshe, wadda aka same ta da wani yaro da ake kyautata zaton nata ne, sojojin sun tare ta ne a lokacin da suke sintiri a kewayen Ngoshe a jihar Borno.
Hakan na kunshe ne a wani sako da rundunar ya wallafa a shafin Twitter a safiyar Laraba.
Sakon ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Dakarun 26 Task Force Brigade da ke sintiri a kewayen Ngoshe a jihar Borno a ranar 14 ga watan Yuni 2022 sun gano wata mata Mary Ngoshe da danta. Ana kyautata zaton tana daya daga cikin ‘yan matan da aka sace daga GGSS Chibok a 2014. Ana ci gaba da bincikarta.”
A wani lokaci cikin shekarar 2014, tsagerun Boko Haram sun shiga makarantar sakandare ta Chibok, inda suka sace wasu 'yan mata 'yan makaranta.
Jigawa: Kotu ta daure masu garkuwa da mutane tsawon shekaru 28 bisa sace yarinya
A wani labarin, Babbar Kotun Jihar Jigawa mai zamanta ta a Dutse, babban birnin jihar ta yanke wa wasu masu garkuwa da mutane uku hukuncin daurin shekaru 28 da watanni biyar a gidan yari ba tare da zabin tara ba.
An samu wadanda ake tuhumar da laifin yin kutse, hada baki da kuma sace wata yarinya mai suna Fatima Abdirrahman, dake karamar hukumar Taura ta jihar, inji Leadership.
Da yake jawabi yayin yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai shari’a M.A Abubakar, ya ce bayan gabatar da shaidu uku ta bakin lauya mai shigar da kara, kotun ta gamsu da cewa babu shakka wadanda ake zargin sun aikata laifin.
Asali: Legit.ng