Da Dumi-Dumi: Sojoji sun ragargaji yan ta'addan ISWAP, Sun tashi kasuwa da sansanonin su a Borno

Da Dumi-Dumi: Sojoji sun ragargaji yan ta'addan ISWAP, Sun tashi kasuwa da sansanonin su a Borno

  • Jami'an tsaro sun yi nasarar halaka yan ta'addan kungiyar ISWAP da dama a yankin Gurzum da ke jihar Borno
  • Hukumar sojojin Najeriya, ranar Laraba da safe, ta bayyana cewa dakarun sun lalata kasuwa da sansanin yan ta'addan yayin samamen
  • Hakanan Sojojin tare da haɗin guiwa dakarun CJTF sun kwato makamai da wasu kayan amfanin yan ta'adda

Borno - Hukumar sojojin Najeriya ta bayyana cewa dakarun tsaro sun samu nasarar halaka yan ta'addan kungiyar ISWAP da dama a yankin Gurzum na jihar Borno.

Hukumar ta ce rundunar Operation Desert Sanity da haɗin guiwar dakarun haɗaka na Civilian Joint Task Forces sun tashi kasuwa da wasu sansanonin yan ta'addan a yankin.

Sojoji sun halaka yan ta'adda a Borno.
Da Dumi-Dumi: Sojoji sun ragargaji yan ta'addan ISWAP, Sun tashi kasuwa da sansanonin su a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Wannan na ƙunshe a wani rubutu mai haɗe da hotuna da hukumar sojojin Najeriya ta saki a shafinta na tuwita ranar Laraba da safe.

Kara karanta wannan

Kano: Yadda 'Dan Ta'addan ISWAP ya Samu Gidan Zama, Ya Siya Filaye 5 da Taimakon Jami'in Hisbah

Ta ce a kokarin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa jami'an tsaron ba tare da gajiya wa ba suna cigaba da kai wa yan ta'addan zafafan hare-hare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari, hukumar sojin ta ce jami'an tsaron sun kuma yi nasarar kwato manyan makamai, da sauran kayan aikin yan ta'addan, yayin wannan ɗauki ba daɗin.

A sanarwan Tuwita da hukumar sojin ta fitar wanda ya ƙunshi hotunan gawarwakin wasu yan ta'addan da sansanin su da aka lalalata, ta ce:

"A cigaba da hana yan ta'adda sakat da rundunar Operation Desert Sanity ke yi tare da taimakon CJTF sun samu gagarumar nasara a ranar 14 ga watan Yuni, 2022.
"Sun yi nasarar halaka yan ta'addan ƙungiyar ISWAP da dama a yankin Gurzum na jihar Borno. Kasuwar yan ta'addan da sansanonin su sun tashi aiki kuma sun kwato makamai da sauran kayan amfani."

Kara karanta wannan

Sojoji da yan sanda sun yi kazamin artabu da yan bindiga a hanyar Kaduna-Abuja, rai ya salwanta

A wani labarin na daban kuma Sojoji sun gano wata mata da Boko Haram suka sace tun 2014

Dakarun runduna ta 26 Task Force Brigade, a ranar Talata, sun gano wata wata Mary Ngoshe, wacce a cewar rundunar sojin Najeriya, tana daya daga cikin ‘yan matan da aka sace a Chibok tunshekarar 2014.

Ngoshe, wadda aka same ta da wani yaro da ake kyautata zaton nata ne, sojojin sun tare ta ne a lokacin da suke sintiri a kewayen Ngoshe a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262