Yan Boko Haram sun kashe yan gwan-gwan guda 55 a Borno, Kwamishanan Yan sanda

Yan Boko Haram sun kashe yan gwan-gwan guda 55 a Borno, Kwamishanan Yan sanda

  • Gwamnatin jihar Borno ta koka kan yadda yan bindiga suke kashe yan gwan-gwan masu shida daji neman karafuna
  • Kwamishanan yan sandan jihar Borno yace cikin makonni uku an kashe yan gwan-gwan hamsin da biyar
  • Yan Boko Haram/ISWAP har ila yau basu daina hallaka fararen hula a Arewa maso gabashin Najeriya ba

Maiduguri - Akalla yan gwan-gwan guda 55 suka rasa rayukansu a harin da yan ta'addan Boko Haram suka kai jihar Borno makonni uku da suka gabata.

Kwamishanan yan sandan jihar, Abdu Umar, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai bayan zaman masu ruwa da tsaki kan matsalar tsaro ranar Asabar a Maiduguri.

Masu ruwa da tsakin sun hada da yan sanda, Sojoji, NSCDC, DSS da sauransu.

Kara karanta wannan

INEC ta baiwa Atiku, Tinubu, Kwankwaso mako 1 su mika mata sunayen mataimakansu

An shirya zaman ne don neman mafita daga cikin harin da yan ta'addan ke kaiwa yan gwan-gwan a jihar, rahoton Premium Times.

CP Umar yace yan ta'addan sun kashe yan gwan-gwan 32 a garin Modu dake karamar hukumar Kala-Balge yayinda suka kashe mutum 23 a garin Mukdala dake karamar hukumar Dikwa.

Yace gwamnan jihar, Babagana Zulum, ya baiwan jami'an tsaro umurnin daukar matakai takaita wannan kisan gillan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace:

"Gwamnatin jihar na shawara samar da hanyar magance wadannan matsaloli. Musamman yanzu da yan gwan-gwan suka fara bin motocin mutane suna cire karafuna."
"An kafa kwamitin duba lamarin ta hanyar hana faruwan haka a gaba."

Kwamishanan Yan sanda
Yan Boko Haram sun kashe yan gwan-gwan guda 55 a Borno, Kwamishanan Yan sanda Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

ISWAP Ce Ta Kashe Masu Ibada 38 a Cocin Owo, In Ji NSC

Kwamitin Koli Ta Tsaro a Najeriya, NSC, ta ce Kungiyar Ta'addanci Ta ISWAP ce ta kai harin da aka kai a cocin St Francis da ke Owo, wanda ya yi sanadin rasuwar mutane 38 a ranar 5 ga watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

Rikici: Gwamnan Fintiri ya saka dokar hana fita a kananan hukumomi biyu na jiharsa

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai na gidan gwamnati jawabi bayan taron Kwamitin Kolin Tsaro a Abuja.

Ya bayyana cewa an umurci jami'an tsaro, musamman yan sanda su kama wadanda suka aikata laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: