Kuma a Najeriya: Fasto ya ba da tarihin cocinsa, ya ce tun 1999 ba a dauke musu wuta ba

Kuma a Najeriya: Fasto ya ba da tarihin cocinsa, ya ce tun 1999 ba a dauke musu wuta ba

  • Hedkwatar cocin Living Faith International, Canaanland ta shafe tsawon shekaru 23 tana morar wutar lantarki ba tare da an dauke ba
  • Shugaban cocin, Bishop David Oyedepo ne ya bayyana hakan a yayin da yake wa’azi a cocin nasa da ke jihar Ogun
  • Ya bayyana cewa cocin ta cimma wannan nasara ne ba tare da taimakon gwamnatin tarayya, ta jiha ko ta karamar hukuma ba

Ogun - Shugaban cocin Living Faith, Bishop David Oyedapo ya bayyana cewa ba a taba dauke wutar lantarki ba a hedkwatar cocinsa da ke Ota, jihar Ogun tsawon shekaru 23.

Oyedepo wanda ya bayyana hakan a yayin da yake wa’azi a hedkwatar cocin da ke Ota, jihar Ogun, ya ce sun cimma wannan nasara ne saboda sun zuba jari na dukiyoyi masu yawan gaske.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

Kuma a Najeriya: Fasto ya ba da tarihin daularsu, ya ce tun 1999 ba a dauke musu wuta ba
Kuma a Najeriya: Fasto ya ba da tarihin daularsu, ya ce tun 1999 ba a dauke musu wuta ba Hoto: Living Faith
Asali: Facebook

Sai dai kuma, malamin addinin ya ce sun cimma wannan nasarar ne ba tare da taimakon gwamnatin tarayya, gwamnatin jiha ko ta karamar hukuma ba, jaridar Vanguard ta rahoto.

Jaridar ta rahoto Oyedepo yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ba a taba dauke wutar lantarki a Canaanland ba tun 1999. Ba mu samu gudunmawa daga kowace gwamnati ba a Najeriya imma ta karamar hukuma, jiha ko tarayya.
"Ba wai muna karbar sadaka duk ranar Lahadi bane don cimma haka. Mun zuba jari na dukiya sannan muna da amintattu kuma jajirtattun mutane da ke kula da shi.
“Mun koyar da duniya cewa za ku iya cimma muradanku ta hanyar dogaro da Allah.”

Gabanin zaben 2023: Tashin hankali zai kunno kai a fadin kasar, inji Babban Hafsan Sojoji

A wani labari na daban, mun ji cewa gabannin babban zaben 2023, Shugaban hafsan soji na kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya ya yi hasashen wasu lamura da ka iya tasowa daga bangaren siyasar kasar.

Kara karanta wannan

Samun wuri: 'Yan ta'addan IPOB sun banka wa motar siminti wuta a jihar Kudunci

Yahaya ya bayyana cewa abubuwa na iya tabarbarewa a bangaren siyasa a fadin yankunan kasar.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni a Port Harcourt, da yake jawabi a wani taron kwamandojin rundunar, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng