Da duminsa: Mahaifiyar ‘dan takaran Sanatan Kano AA Zaura ta samu kubuta daga wajen yan bindiga
- Dan takarar kujerar Sanata ya sanar da kubutar mahaifiyarsa da yan bindiga suka yi awon gaba jiya
- A.A Zaura ya bayyana cewa Babarsa Laure ta kubuta daga hannun yan ta'addan ne da safiyar Talata
- Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun addabi al'ummar Arewa maso yammacin Najeriya
Kano - Mahaifiyar dan takaran kujerar Sanata, Abdulkarim Abdulsalam Zaura wanda aka fi sani da A. A Zaura, ta samu kubuta daga wajen yan bindigan da suka sace ta.
AA Zaura na takaran neman kujerar dan majalisar dattawan tarayya mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya.
Dan siyasan a yau Talata, 7 ga Yuni, 2022 ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta samu kubuta.
A jawabin da ya daura a shafinsa na Facebook, yace:
"Cikin ikon ALLAH, ALLAH Madaukakin sarki YA Kubutar da Babata Hajiya Laure Abdulkarim daga hannun wadanda sukayi garkuwa da ita da safiyarnan.
"Babban Godiya ta ga Jami'an tsaro, wadannan bayin ALLAH sunkasa Zaune sun kasa tsaye har Saida suka samu Nasarar Kubutar da Babata daga wannan kangi, Godiya ga: Jami'an Hukumar Farin Kaya,Rundunar Yan sanda da Kuma Sojin kasa na Najeriya Hadida Hukumar Civil defense.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ina Adduar ALLAH YA sakawa kowa da Alheri.
Ya mika godiyarsa ga al'umma bisa damuwar da suka nuna bisa wannan ibtila'i da ta afka masa da iyalinsa.
"Tabbas, Banda kalmomin da zanyi Godiya da irin soyayya da Kaunar da aka nunamin, ta hanyar Alhini, Adduo'i da Kuma kiraye kirayen wayoyi da sakonni. Godiya ga Yan uwana na Siyasa da dimbin Masoya da Magoya baya, Malaman Jihar Kano, Matan Aure da Yan Mata, Matasa bisa ga Adduo'i na fatan Alheri da kubuta. - Nagode"
Da Duminsa: Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC
Garkuwa da Hajiya Laure Zaura
Da safiyar Litinin, 6 ga watan Yuni 2022, wasu miyagu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun dauke tsohuwar Abdulkarim Abdulsalam Zaura.
An yi awon gaba da Hajia Laure Mai Kunu ne cikin tsakar daren Litinin, kafin a kira sallar asuba.
Shugaban karamar hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya bayyanawa jaridar wannan, ya ce sun sanar da jami’an tsaro.
Asali: Legit.ng