Yanzu-yanzu: Matasa sun kashe wani mutumi Musulmi kan zagin Manzon Allah (SAW) a Abuja

Yanzu-yanzu: Matasa sun kashe wani mutumi Musulmi kan zagin Manzon Allah (SAW) a Abuja

Lugbe, Abuja - Wasu matasa a ranar Asabar sun hallaka wani dan kungiyar Bijilante kan zargin kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW) a birnin tarayya Abuja.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

An tattaro cewa an hallaka dan Bijilantin ne a sashen yan Timba dake kasuwar kayan itace a unguwar FHA Lugbe, rahoton Punch.

Wani mai idon shaida yace dan Bijilantin Musulmi ne kuma ya shahara da zagin manzon Allah amma yayi wani sabo da daren jiya.

A riwayar Daily Trust, bayan kalaman batancin, sai ya gudu ya nemi mafaka a Ofishin yan Bijilanti dake kasuwar misalin karfe 1 na rana.

Yanzu-yanzu: Matasa sun kashe wani mutumi Musulmi kan zagin Manzon Allah (SAW) a Abuja
Yanzu-yanzu: Matasa sun kashe wani mutumi Musulmi kan zagin Manzon Allah (SAW) a Abuja Hoto: Abdul Yassar Auwal
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa a wannan lokacin fusatattun matasa suka kure masa gudu suka fito da shi karfi da yaji daga cikin ofishin kuma suka kasheshi kai tsaye, daga baya suka konashi.

Kara karanta wannan

Kano: Mutum 201 na Kwance Rai a Hannun Allah a Asibiti Bayan Shakar Kemikal a Sharada

Wani dan kasuwa a wajen mai suna Halilu yace:

"Sunan mutumin Small Hundaru, wannan ba shine karon farko da zai zagi annabi ba."
"An damkeshi yana kokarin sayen abinci a kasuwa da rana, saboda lokacin da yayi batancin, babu mutane sosai a wajen, sai aka buga masa ice a akai. Sai da aka kwace bindigar hannunsa suka lallasa shi."
"Daga baya suka masa jifa kafin ya gudu ofis. Abokan aikinsa sun gaza kareshi saboda adadin mutanen da suka kure masa gudu. Da ya sume suka zuba masa fetur suka banka masa wuta a gaban ofishinsu."

Rahoton ya kara cewa yan sanda sun harbi mutum uku cikin matasan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: