Duk wanda ya zo Belin ɗan ta'adda ku damƙe shi duk matsayinsa, Ministan Buhari ya fusata

Duk wanda ya zo Belin ɗan ta'adda ku damƙe shi duk matsayinsa, Ministan Buhari ya fusata

  • Ministan Abuja, Mallam Muhanmad Bello, ya bukaci hukumomin tsaro kar su duba matsayin mutum, da ya zo belin me laifi su damƙe shi
  • Ya ce sun samu rahoton cewa wasu manyan mutane na zuwa suna saka baki a saki masu laifi, ba zasu yarda haka ta cigaba da faruwa ba
  • Ministan ya roki al'umma su taimaka wa hukumomin tsaro da bayanan duk wanda suka ga ya kuɓutar da me laifi

Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Muhammed Bello, ya buƙaci hukumomin tsaro su cafke duk wanda ya zo neman a ba shi beli wani mai aikata manyan laifuka.

Ministan ya yi wannan kira ne ranar Alhamis a wurin taron mako-mako da ake shirya wa Ministoci don bayanin ayyukan su, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tinubu ya saki sabon Bidiyo, ya faɗi inda zai nufa idan ya sha ƙasa a zaɓen fidda gwanin APC

Bello ya bayyana cewa yin hakan wani ɓangare ne a kokarin da suke yi wajen tsaftace birnin tarayya daga aikata manyan laifuka.

Ministan FCT Abuja, Muhammad Bello.
Duk wanda ya zo Belin ɗan ta'adda ku damƙe shi duk matsayinsa, Ministan Buhari ya fusata Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ministan ya kuma ƙara da cewa harajin da ake karɓa a babban birnin tarayya wato Abuja, ana tsammanin nan gaba zai zarce wanda jihar Legas ke tarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mallam Muhammed Bello ya sanar da cewa a yanzun Birnin ya na tattara biliyan N200bn shekara-shekara daga karɓan Haraji, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Wane mataki gwamnati ke ɗauka kan tsaron Abuja?

Da yake jawabi kan matakan kawo karshen aikata manyan laifuka a Abuja, Ministan ya ce ya zama wajibi su ankarar da jami'an tsaro saboda sun sami rahoton yadda manyan mutane masu matsayi ke zuwa kubutar da masu laifi.

Ya kuma yi kira ga mazauna Abuja su tona asirin duk wanda ke kokarin kubutar da masu laifi ta hanyar kai rahotonsu ga hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Gumi ya bukaci FG ta kafa ma'aikatar harkokin makiyaya don jin kokensu

Bello ya koka cewa a halin yanzun gidan gyaran hali uku da ke Abuja duk sun cika taf kuma ba za'a ƙara ko mutum ɗaya da aka kama da laifi ba.

A cewarsa, idan Kotu ta tabbatar da laifin wani a Abuja sai dai a tura shi zuwa Gidan Yarin Suleja a jihar Neja, yayinda FCT ke shirin samar da Yari na musamman da za'a rinka ɗaure kananan yara.

A wani labarin kuma APC ta gamu da babban cikas, Ɗan takarar gwamna da dubbannin magoya baya sun fice daga jam'iyyar

Yayin da APC ke shirin zaben fidda ɗan takararta na shugaban ƙasa, jam'iyyar ta yi babban rashi na mambobinta a jihar Oyo.

Ɗan takarar gwamna da ya sha ƙasa, Chief Adebayo Adelabu, ya jagoranci masoyansa sun koma Accord Party.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: