Bani da niyyar shiga addinin Musulunci, Dan wasan Nollywood Jim Iyke

Bani da niyyar shiga addinin Musulunci, Dan wasan Nollywood Jim Iyke

  • Jim Iyke ya yi tsokaci game da labarin dake yawo cewa ya karbi addinin Musulunci kuma ya sauya sunansa
  • Dan wasan Nollywood hotunan da aka gani dake nunashi da wasu Musulmai Fim ne suke shiryawa
  • Yace yana kan shirya wani Fim kan tsattsaurin ra'ayin addinin Musulunci a kasar Ghana

Dan wasan kwaikwayon Nollywood, Jim Iyke, ya yi watsi da rahotannin dake yawo a kafafen sada zumunta cewa ya sauya addini daga Kirista zuwa Musulunci.

Wani rahoto ya yadu ranar Laraba cewa dan diraman ya shiga addinin Musulunci kuma Musulmai a fadin kasa sun tayashi murna.

Jim Iyke a ranar Alhamin ya yi jawabin karyata rahotannin a bidiyon da ya saki a shafinsa an Instagram.

Jim Iyke
Bani da niyyar shiga addinin Musulunci, Dan wasan Nollywood Jim Iyke Hoto: Jim Iyke

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kada ka 'kakaba mana dan takaran shugaban kasa, Mataimakin Shugaban APC ga Buhari

A cewarsa, ko kadan ba shi niyyar shiga addinin Islama.

Yace hotunan da aka gani na wani Fim ne da suka dauka kan ta'addanci a Ghana.

A cewarsa:

"Bari inyi gaggawan martani da wani jita-jita. Na yi wani Fim a Ghana kuma kan tsattsaurin ra'ayn addini ne, wani ya dauki hotunan Fim din yace na Musulunta."
"Ina mai girmama dukkan addinai kuma bani da niyyar sauya addini. Ban san dalilin da ya wasu zasu yi haka ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel