Deleget din PDP dan jihar Kaduna ya rabawa alummarsa sama da N10m cikin abinda ya samu

Deleget din PDP dan jihar Kaduna ya rabawa alummarsa sama da N10m cikin abinda ya samu

Tanko Sabo, wani Deleget dan jihar Kaduna ya bayyana cewa ya kashewa al'ummar kudi akalla N10m cikin kudin da ya samu a zaben fidda gwanin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yayin yakin neman zabe, Deleget din ya yiwa al'ummar yankinsa alkawarin cewa duk kudin da ya samu zai raba da su a karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.

Bayanai kan kudin da ya raba, yace ya biya kudi N6.9 million kudin WAEC da NECO na dalibai marayu 150 da marasa galihu.

Ya kara da cewa ya biya mambobin kwamitin da ya nada su biya kudin jarabawar su biyar kowa N100,000.

Sabo ya kara da cewa ya kashe N3.2m wajen sayan Jesin kwallo guda 42, safuna, rigunan kwallon don inganta wasanni a yankin.

Ya kara da cewa ya baiwa shugabannin PDP a gundumarsa kudi N1.3m.

Kara karanta wannan

Deliget din PDP ya sadaukar da dukkan kudin da ya samu ga al'ummarsa, ya biya wa yara kudin makaranta

Ya kara da cewa ya baiwa dattawa da maroka N350,000 kuma ya baiwa wani Danladi N100,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel