Bayan kwana 40, 'dan Najeriya da ya tuko babur daga London ya iso Legas, hotunansa sun bayyana

Bayan kwana 40, 'dan Najeriya da ya tuko babur daga London ya iso Legas, hotunansa sun bayyana

  • Kunle Adeyanju, wani jajirtaccen 'dan Najeriya ne wanda a tsakiyar Afirilu ya dauki haramar isowa Legas daga Landan a babur, wanda daga karshe ya iso kasarsa
  • Masu babura da mutanen dake bibiyar tafiyarsa sun tarbe sa hannu bibbiyu cike da farin ciki yayin da ya isa lami lafiya
  • Mutumin wanda ya fuskanci kalubale kala-kala ya yanke shawarar fara tafiyar ne a matsayin wani bangare na End polio din shi

Legas - An fara wannan tafiyar kan titi mai cin rai ne a 19 ga watan Afirilu sannan aka kammala a ranar 29 ga watan Mayu wanda wani mai babur Kunle Adeyanju ya fara kuma ya iso Najeriya.

Jajirtaccen mutumin ya kwashe kwanaki 40 a kan hanya daga Landan zuwa Legas a kan babur da yake tukawa da kansa domin end polio.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: EFCC ta sake bankado wata badakalar biliyan N90 kan Akanta-Janar, ya zama biliyan N170

A gaba daya tafiyar, mai amfani da yanar gizo a matsayin Savvy Kunle ya dauki aniyarsa tare da kara yawan mabiya gami da yin wallafe-wallafe a kan duk wata gaba da ya tsaya, kalubalen da ya fuskanta, har ma da kalubalen da mutane suka jefa sa.

Bayan kwana 40, 'dan Najeriya da ya tuko babu daga London ya iso Legas, hotunansa sun bayyana
Bayan kwana 40, 'dan Najeriya da ya tuko babu daga London ya iso Legas, hotunansa sun bayyana. Hoto dga @Badgang_ng
Asali: Twitter

A wani bidiyo da ya yadu, 'dan Najeriyan mai babur Kunle Adeyanju ya ce, yayin da ya isa iyakar Seme, wani wuri tsakanin iyakar Najeriya da Benin, tukin minti talatin daga Badagry a titin jar kasa tsakanin Legas da Kwatano, Kunle ya samu tarba hannu bibbiyu daga masu babura da mutanen da suka bi tafiyarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An dauki hotonsa da jami'an kula da shige da fice na Najeriya da tarin mabiyansa, kamar yadda aka gani da hotunan da Punch ta wallafa.

'Yan Najeriya sun taya shi murna

Kara karanta wannan

EFCC ta gano sabbin N90bn da AGF Ahmed Idris ya wawure, ya tona asirin minista da wasu jiga-jigan gwamnati

Jessica Chinaza Sunday ta ce: "Ubangiji da girma yake, an kafa tarihi a Najeriya da shi, ina taya mutanen kauyensa, yankinsa, karamar hukumarsa, jiharsa da Najeriya baki daya."

Regina Osakwe ta ce:

"Muna godiya ga Ubangiji da jinkan da yasa a tafiyar nan har tayi armashi barka da zuwa, kuma ka koya mana yadda ake amfani da babur don mu bika mu koma Landan... Za a iya kiran hakan da tsira a tukin babur."

Emmanuella Ezoke ta ce:

"Yallabai ina taya ka murna. Sannu da zuwa. Ka taimaka idan za ka koma Landan ka bari in bi ka saboda ina so in ware daga wannan kasar.
"Dama Landan ba da nisa sosai haka. Ina so in zauna kusa da kai idan zaka koma gida. Kada ka ba kowa wuri na saboda ni na fara magana kafin 'yan bakin ciki su batamin shiri."

Igbinedion ya ce:

"Ina taya ka murna, na jinjina maka babban zakin Afirka, na samu labarin da zan ba wa yarana, idan an tambaye su, waye 'dan Najeriya na farko ko 'dan Afirka na farko da ya taba tafiya Landan zuwa Najeriya a babur, zan ce sunansa Kunle Adeyanju, alamu na nuna ya kashe kudi sosai."

Kara karanta wannan

Inyamurai ne: Gwamna ya bayyana masu hallaka mutane a yankin Kudu maso Gabas

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng