Yanzu-yanzu: Kungiyar Malaman makarantun Poly sun janye daga yajin aiki, sunce a koma aji

Yanzu-yanzu: Kungiyar Malaman makarantun Poly sun janye daga yajin aiki, sunce a koma aji

  • An umurci daliban makarantun fasaha da malamansu su koma aji ranar Litnin saboda yajin aiki ya kare
  • Malaman sun gabatar da wasu bukati guda shida amma ga dukkan alamun gwamnatin tarayya ta amsa daya
  • Ministan kwadaga a farko makon nan yace gwamnati zata biya malaman makarantun gaba da sakandare kudin bashin da suke bin gwamnati

Abuja - Kungiyar Malaman makarantun fasaha na tarayya watau ASUP ta umurci Lakcarorin Poly su koma bakin aiki ranar Litnin 30 ga Mayu, 2022 .

Wannan ya biyo bayan amsa bukata daya cikin jerin bukatu shida da kungiyar ta gabatarwa gwamnatin tarayya.

Zaku tuna cewa ranar 16 ga Mayu, 2022, ASUP ta sanar da shiga yajin aikin gargadi na makonni biyu.

A bayan mun kawo muku cewa Gwamnatin tarayya ta fara biyan malaman jami'o'i na Poly da na kwalejin Ilimi dake fadin tarayya kudin karin mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe makiyaya 4, sun sace shanaye 60 a Anambra

Yayinda Malamn jami'a suka ce wannan bai cikin bukatunsu, na Poly suce su suna so.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ASUP
Yanzu-yanzu: Kungiyar Malaman makarantun Poly sun janye daga yajin aiki, sunce a koma aji Hoto: aitonline
Asali: UGC

Punch ta ruwaito cewa Kakakin kungiyar ASUP, Abdullahi Yahaya, a jawabin da ya rattafa hannu yace::

"Zamu kammala yajin aiki ranar 29 ga Mayu, 2022... Saboda haka kungiya na kira ga mambobi su koma bakin ayyukansu ranar 30 ga Mayu, 2022, kuma muna sa ran gwamnati za tayi amfani da wannan dama wajen amsa sauran bukatun."

Legit Hausa ta tuntubi wani dalibi mai karatu kwalejin fasaha ta jihar Kaduna watau Kadpoly, AbdulRaqib Ishaq, kan halin da dalibai suka shiga kan wannan jawabi.

Ya bayyana mana cewa ba karamin farin cikin samun wannan labari yayi ba saboda kai tsaye zasu cigaba da jarabawarsu.

Yace:

"Da yawa cikin Malamanmu sun dawo aiki kuma sun cigaba da ayyukansu. Dalibai kuwa duk da dadin dawowa makaranta basu ji dadi ba saboda karatun da sukayi don jarabawar a baya ya zube."

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Dalibai zasu kai shekarar 2023 a gida saboda ba zamu janye daga yajin aiki ba, ASUP

A baya, shugaban kungiyar malaman makarantun Poly na Najeriya, Anderson Ezeibe, yace babu alamun za'a janye daga yajin aiki a wannan shekarar ta 2022.

Yayin jawabi a ganawar da mambobin kungiyar suka yi a Kwalejin fasahar tarayya dake Ilaro, jihar Ogun, Ezeibe ya yi gargadin cewa gwamnatin tarayya har yanzu bata biya musu bukatunsu ba, duk da yarjejeniyar da sukayi shekara daya yanzu.

A riwayar Punch, Ezeibe ya ce yajin aikin gargadi na makonni biyu da suka shiga kwanan nan suna yi ne don nunawa gwamnati bacin ransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng