Rayuwata na cikin hadari a Kurkuku, Abba Kyari ya bayyanawa kotu
- Abba Kyari ya sake gurfana gaban kotu dake birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, 26 ga Mayu, 2022
- Babban jami'in dan sandan da aka dakatar yace ana yiwa rayuwarsa barazana a kurkuku Kuje, inda aka jefashi
- Karo na biyu, lauyoyinsa sun gabatar da bukatan a sake shi don ya tafi gida sannan a cigaba da karar, watau a bashi beli
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Dakataccen mataimakin kwamishanan yan sanda, Abba Kyari, ya bukaci kotu ta bashi beli saboda rayuwarsa na fuskantar hadari cikin gidan yari.
Lauyansa, Dr. Onyechi Ikpeazu (SAN), ya gabatarwa babbar kotun tarayya bukatar a ranar Alhamis, rahoton Vanguard.
Ya ce sun bukaci hakan ne saboda rayuwar Abba Kyari na cikin hadari.
Lauyan ya bukaci kotu ta taimaka ta baiwa Kyari beli saboda kada a kashe shi.
Amma lauyan gwamnati, Joseph Nbona, ya nuna rashin amincewarsa da hakan in da yace bai samu labarin haka ba kuma ba'a bashi nashi kwafin kudirin ba, a kotu kadai ya ji ana fadi.
A riwayar ChannelsTV, Alkali mai shari'a, Emeka Nwite, ya yanke cewa za'a dage zaman don bangarorin biyu su tattauna tsakaninsu kuma abi tsari.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Alkali daga bisani ya dage zaman zuwa ranar 14 ga Yuni, 2022 don sauraron lamarin belin.
Abba Kyari ya sha da kyar, saura kiris masu fushi da shi su hallaka shi a gidan yari
Jami'an gidan yari suna tunanin mayar da jami'in 'dan sanda Abba Kyari daga gidan yarin Kuje zuwa hannun jami'an tsarin farin kaya bayan wasu daga cikin abokan zamansa sun yi yunkurin halakasa sakamakon zarginsa da rashin gaskiya wajen bada cin hanci don a samar musu da kwangila a lokacin da yake kan aiki.
Kamar yadda wasu takardun cikin gida da Premium Times ta samu damar gani suka bayyana, an kai masa harin ne a 4 ga watan Mayu, watanni bayan kama Kyari da laifin safarar miyagun kwayoyi. Maharansa sun kai kimanin 190, a cewar wani jami'i, kuma da yawansu an kai su gidan yarin ne saboda harkallar miyagun kwayoyi.
Asali: Legit.ng