Emefiele yana nan: Ba mu san da labarin tunbuke Gwamnan babban banki ba inji CBN

Emefiele yana nan: Ba mu san da labarin tunbuke Gwamnan babban banki ba inji CBN

  • Labarin sauke gwamnan bankin CBN da yake ta yawo a tsakiyar makon nan sam ba gaskiya ba ne
  • Har dai zuwa yanzu Godwin Emefiele ne yake rike da babban bankin Najeriya, ba a tunbuke shi ba
  • A dokar kasa, ana bukatar rinjayen Sanatoci kafin a iya sauke gwamnan na CBN daga kujerarsa

Abuja - Babban bankin Najeriya na CBN ya ce bai da masaniyar cewa an sauke gwamnan bankin, Godwin Emefiele kamar yadda rade-radi su ke yawo.

Jaridar The Nation ta tuntubi Mai magana da yawun bankin CBN, Osita Nwanisobi, wanda ya nuna cewa wannan labari bai da tushe ko makama.

A ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, 2022, Mista Nwanisobi ya ce shi ma ya karanta wannan rahoto kamar yadda kowa ya karanta a kafafen yada labarai.

Kara karanta wannan

Zulum: Allah ke ba da mulki, ba zan roki wani ya dauke ni abokin takarar shugaban kasa ba

“Ni ma na ji labarin kamar yadda ku ka ji. Maganar gaskiya ban da masaniyar wannan lamarin.”

- Osita Nwanisobi

Karya ce ake yadawa - CBN

A wani makamancin rahoto da ya fito daga Punch a jiya, an tabbatar da cewa maganar tsige Godwin Emefiele ba komai ba ce face jita-jitar karya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar ta nemi jin ta bakin kakakin bankin, amma ba ta iya samun shi ta wayar salula ba.

Godwin Emefiele
Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Amma majiyoyi dabam-dabam sun rahoto Nwanisiobi a madadin bankin CBN yana cewa ba ta tabbata ba cewa Godwin Emefiele zai bar kujerarsa.

Daily Trust ta bi diddikin labarin, ta kuma fahimci ba gaskiya ba ne. Rahoton da ta fitar ya ce a kasar Aljeriya ne aka sauke gwamnan babban banki.

A ranar Litinin, shugaban Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune ya tunbuke Rostom Fadli daga kujerarsa, duka-duka bai wuce shekara biyu a ofis ba.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya bayyana irin yadda yake matukar son gaje Buhari, ya ce ba wasa yake ba

Sai dai a tsarin mulkin Najeriya, dole sai majalisar dattawa ta amince kafin a iya tunbuke gwamnan.

Godwin Emefiele ya shiga APC

Rahoton Punch ya nuna cewa gwamnan babban bankin cikakken ‘dan jam’iyyar APC ne. Emefiele ya yi rajista da APC a karamarsa ta Ika ta Kudu, a jihar Delta.

Shugaban APC na mazabar, Nduka Erikpume ya shaidawa ‘yan jarida ta waya cewa sun yi wa gwamnan babban bankin rajista a matsayin ‘dan jam’iyya.

Ina Oduah ta samu satifiket?

An ji labari cewa a shekarar 1982/83 aka tura Stella Adaeze Oduah zuwa jihar Legas domin tayi wa Najeriya hidima, amma a karshe ba ta karasa aikin ba.

Duk da Sanata Stella Adaeze Oduah ba ta kammala yi wa kasar ta hidima kamar yadda doka ta tanada ba, sai ga shi ta na da satifiket da ake da ta-cewa a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng