Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra
- Kungiyar Kiristocin Najeriya ta fitar da jawabi kan kisan mace mai juna biyu da yaranta a jihar Anambra
- Kungiyar addinin ta yi Alla-wadai da abinda yan ta'adda sukayi kuma ta yi kira ga shugabanni su dau mataki
- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, har yanzu mutane na sauraron jawabinsa kan abinda ya faru
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kaduna - Kungiyar Kiristocin Najeriya, shiyyar jihar Kaduna (CAN) ta yi Alla-wadai da kisar wata mata yar Arewa mai juna biyu tare da 'yayanta hudu a jihar Anambra, Kudu maso gabas.
Tsagerun yan bindiga da ake zaton yan kungiyar awaren IPOB ne suka kai farmakin inda suka hallaka mutane 12 ciki harda matar mai tsohon ciki, Harira Jibril da yaranta su hudu.
Wannan lamari ya faru ne a karamar hukumar Orumba North karshen makon da ya gabata.
Shugaban CAN na Kaduna, Joseph Hayab, ya ce ran kungiyar ya baci bisa wannan abu da ya faru.
A jawabin da ya fitar yace:
"Rayuwar dan Adam a kasar nan tayi arha saboda kowani sashe na da yan ta'adda."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"CAN na yi kisan Fatima, jaririn dake cikinta da yayanta hudu da yan ta'adda sukayi a Anambra matsayin abu mara kyau ga zaman lafiya da hadin kan Najeriya."
"CAN na kira ga Gwamnatin tarayya ta nemo makasan Fatima da dukkan wadanda aka yiwa kisan gilla a Najeriya."
Ina gab da haukacewa: Mijin mata da 'ya'ya 4 da IPOB suka kashe ya magantu
Mijin matar da aka kashe ya bayyana cewa ya ji kamar ya yi hauka sakamakon tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki.
Mijin matar kuma uba ga yara hudun da aka kashe a harin ya shaida wa BBC cewa an kashe iyalin nasa ne a lokacin da suke kan hanyar su ta dawowa daga ziyarar da suka kai a yankin Orumba ta arewa a jihar Anambra.
Asali: Legit.ng