Kisar Ƴan Arewa a Kudu: Kada Ku Fara Faɗan Da Ba Zai Ƙare Ba, IPOB Ta Yi Wa Ƙungiyoyin Arewa Martani

Kisar Ƴan Arewa a Kudu: Kada Ku Fara Faɗan Da Ba Zai Ƙare Ba, IPOB Ta Yi Wa Ƙungiyoyin Arewa Martani

  • Haramtaciyyar kungiyar yan aware masu neman kafa kasar Biafra, IPOB ta gargadi Hadakar Kungiyoyin Farar Hula na Arewa, CNG, kan barazanar da ta yi game da kashe hausawa a Kudu
  • CNG ta ce ba za ta cigaba da zuba ido tana kallo ana yi wa hausawa kisar gilla a yankin kudu ba don haka idan abin ya cigaba za ta dauki mataki
  • IPOB, a martaninta ga CNG ta yi barazanar cewa muddin kungiyoyin na arewa suka taba ibo a yankinsu tabbas za a fara wani rikici da ba a san karshensa ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kungiyar Masu Neman Kafa Biafra IPOB ta gargadi Gamayyar Kungiyoyin Arewa, CNG, dangane da fara kashe yan kabilar Ibo, tana mai cewa kada a fara fadar da ba za ta kare ba.

Kara karanta wannan

Ina tsananin bukatar aure cikin gaggawa, Wata Jarumar masana'antar Fim a Najeriya ta cire kunya

Kungiyar ta bayyana hakan ne a matsayin martani kan barazanar da CNG ta yi game da kashe mata yan uwa a yankin kudu maso gabas kamar yadda The Punch ta rahoto.

Kisar Ƴan Arewa a Kudu: Kada Ku Fara Faɗan Da Ba Zai Ƙare Ba, IPOB Ta Yi Wa Ƙungiyoyin Arewa Martani
Kisar Bahaushiya Da Yayanta 4: Kada Ku Fara Faɗan Da Ba Zai Ƙare Ba, IPOB Ta Yi Wa Ƙungiyoyin Arewa Martani. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Arewa ba za ta zuba ido tana kallo ana kai wa mutanenta hari ba, don haka bata ta zabi illa daukan mataki idan aka sake tsokananta ko kai wa mutanenta hari.
"Kame baki da arewa ke yi ba tsoro bane ko rashin sanin hanyar da za mu bi mu rama abin da ake mana, wadanda ke neman mu da rikici su san cewa ba za mu cigaba da zuba ido muna kallo ba," in ji kakakin CNG, Abdulazeez Sulaiman."

Martanin IPOB ga sakon CNG kan Kisar Yan Arewa a Kudu

Amma Sakataren Watsa Labarai na IPOB, Emma Powerful, cikin wata hira da The Punch ta yi da shi a daren ranar Talata ya ce ba su da hannu a kisar bahaushiyar da yayanta hudu.

Kara karanta wannan

Zulum: Allah ke ba da mulki, ba zan roki wani ya dauke ni abokin takarar shugaban kasa ba

Wani sashi cikin kalaman Powerful ya ce, "Muna da abubuwa da yawa a gabanmu balantana mu tsaya amsa wannan kungiyar mai suna CNG saboda ba su ba komai bane; muna jiran su fara kashe-kashe a Najeriya za su ga matsayin mu.

"Za mu cigaba da neman kafa Biafra ba da tada hankali ba amma idan ba za su janye bata garin da suka turo yankin mu suna tunanin za mu tsere mu bar musu yankin, wasa suke. Su fara wannan fadar za su ga yadda abin zai cigaba.
"IPOB bata da hannu a kissar bahaushiyar nan da yaranta a ranar Lahadi kuma muna tir da mummunan lamarin da wasu bata gari da yan arewa ke daukan nauyi suka aikata."

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164