An ki cin biri, an ci dila: Yadda sabon AGF ke da jikakkiyar tuhumar rashawa da EFCC

An ki cin biri, an ci dila: Yadda sabon AGF ke da jikakkiyar tuhumar rashawa da EFCC

  • An gano cewa sabon akanta janar da Buhari ya nada domin maye gurbin Ahmed Idris yana da jikakkiyar tuhumar rasahawa tare da hukumar EFCC
  • Bayanai sun fallasa yadda ya dinga wabtarar kudin kasa yayin da yake aiki da ma'aikatar tsaro kuma yana matsayin daraktan kula da kudi da asusai
  • Wani jami'i da ya bukaci a adana sunansa, ya sanar da cewa yanzu haka EFCC na rike da wasu kadarorin sabon akanta janar Nwabuoku

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Anamekwe Nwabuoku, sabon akanta janar wanda aka nada domin kula da ofishin akanta janar na tarayya, yana da jikakkiyar tuhuma ta zargin rashawa wanda hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ke yi masa.

Idan za a tuna, an nada Nwabuoku ya maye gurbin Ahmed Idris a ranar Lahadi bayan dakatar da Idris da aka yi kuma yana hannun hukumar EFCC kan zarginsa da almundahanar kudi har N80 biliyan.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Muka Yi Dirar Mikiya a Gidan Okorocha, EFCC Ta Magantu

An ki cin biri, an ci dila: Yadda sabon AGF ke da jikakkiyar tuhumar rashawa da EFCC
An ki cin biri, an ci dila: Yadda sabon AGF ke da jikakkiyar tuhumar rashawa da EFCC. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma rahoto daga EFCC ya bayyana cewa sabon AGF din ana tuhumarsa da laifukan rashawa.

Rahoton ya kara da cewa, wasu daga cikin zargin da ake masa sun hada da kara wa kansa kudi kan albashinsa a MDA da yayi aiki a baya.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wasu daga cikin kadarorin da ya mallaka ta wannan damfarar duk suna hannun hukumar EFCC.

Daya daga cikin majiyoyin da ya bai wa Daily Nigerian tabbaci, ya ce laifin da ake zarginsa da su ya yi shi ne yayin da yake daraktan kudi da asusu, DFA, a ma'aikatar tsaro inda aka ce ya azurta kansa da kudin tsaron cikin gida.

Ana zarginsa da hannu cikin wasu lamurran damfara tare da amfani da GIFMIS wurin satar albashin ma'aikatan tarayya.

Kara karanta wannan

An gudu ba'a tsira ba: An bankado wani sirrin cin hanci na sabon Akanta Janar da Buhari ya nada

GIFMIS wani tsari ne na kula da kasafi da asusu. Ana amfani da shi wurin sabunta tsarikan ayyukan ma'aikatan tarayya tun daga shekarun 2000s.

Nwabuoku ya yi amfani da tsarin inda yayi rub da ciki kan wasu kudade.

A yayin da aka nemi jin ba'asin abunda yasa gwamnatin tarayya ta nada mutumin da EFCC ke tuhuma da rashawa, wani babban jami'i a fadar shugaban kasa ya ce Nwabuoku ne babban jami'i a ofishin mai bin Ahmed Idris.

"Ba mukaddashin AGF aka nada shi ba, an nada shi ne ya kula da ofishin saboda shi ne babban darakta a ofishin," jami'in ya bayyana.

Nwabuoku yana da watanni kalilan na aiki kafin ya yi ritaya a matsayin ma'aikacin gwamnatin tarayya.

EFCC ta yi ram da tsohon MD na NDDC kan zargin handamar N47bn

A wani labari na daban, jami'an hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, a ranar Laraba sun yi ram da tsohon manajan daraktan hukumar cigaban Neja Delta, NDDC, Nsima Ekere.

Kara karanta wannan

Amma dai tela bai kyauta ba: Dinkin rigar wani yaro ya girgiza intanet, ana ta cece-kuce

Ana zargin tsohon shugaban hukumar NDDC din da waskar da makuden kudade da suka kai N47 biliyan ta hanyar amfani da 'yan kwangila masu rijista na hukumar.

Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwajaren ne ya tabbatar wa da Channels TV hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng