Har yanzu ina APC, ban koma PDP ba: Sanata Danjuma Goje
- Tsohon gwamnan jihar Gombe ya karyata rahotannin cewa yana kokarin komawa jam'iyyar PDP
- Danjuma Goje ya ce ba da izininsa aka sanya suna da hotonsa a takardar kuri'ar takara Sanata a PDP
- Goje ya lashi takobin shigar da PDP kotu idan bata fito ta bashi hakuri kan wannan abu ba
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje, a ranar Litnin, ya yi watsi da labarin cewa ya yi takara a zaben fidda gwanin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da akayi a jihar.
Goje yace har yanzu shi dan jam'iyyar All Progressives Congress APC ne.
Ya bayyana haka a jawabin da hadiminsa, Ahmed Isa, ya fitar a Abuja.
Yace:
"Sanata Danjuma Goje ya samu labarin rahotanni a kafafen yada labarai cewa yayi musharaka a zaben fidda gwanin Sanatan PDP da akayi ranar Litinin, 23 ga Mayu, 2023."
"Sanata Goje dan jam'iyyar APC ne kuma Sanatan APC. Ba dan PDP bane. Bai yi takara a zaben fidda gwanin PDP ba. Hotunan Goje da aka gani a takardar kuri'a sharrin yan adawa ne."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yana Sanatan APC amma sunan Danjuma Goje ya bayyana wajen zaben fidda gwanin PDP
Wakilan zaben shugaba wadanda akafi sani da deleget na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Gombe sun ga abin mamaki ranar Litnin wajen zaben fidda gwani.
Yayinda suka shiga kada kuri'unsu, sai suka ga Sanatan APC mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje, cikin jerin yan takaran, rahoton Leadership.
Zaku tuna cewa an yi rade-radin Sanata Danjuma Goje zai sauya sheka daga APC zuwa PDP sakamakon rashin jituwar dake tsakninsa da Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya.
Tuni dai uwar jam'iyyar APC ta shirya zaman sulhu tsakanin jiga-jigan siyasan kuma hakan ya hana Danjuma Goje komawa PDP.
Amma a ranar Litinin yayi zaben fidda gwanin PDP, sunan Danjume Goje ya bayyana cikin yan takara.
Asali: Legit.ng