Daga karshe, Matar da ta dau juna biyu tsawon shekara 6 ta haihu

Daga karshe, Matar da ta dau juna biyu tsawon shekara 6 ta haihu

  • Abin da ban mamaki, wata mata yar Najeriya ta haihu bayan shekara shida tana dauke da juna biyu
  • Taiwo Lawal, yar shekara 37 ta bayyanawa Legit a hira cewa ta fara fuskantar matsala ne tun tana watanni uku da daukar cikin
  • A cewarta, har ta fara tunanin kashe kanta saboda bakin cikin halin da take ciki

Wata mata yar Najeriya mai suna Taiwo Lawal ta haihu daga karshe ranar 11 ga watan Mayu, 2022 bayan kwashe shekaru shida tana dauke da juna biyu.

A hirar da tayi da Legit.ng, Taiwo ta bayyana cewa har yanzu tana mamakin cewa ta haifi jaririya.

A jawabin da tayi, tace watanni uku da daukar cikin tayi wani mugun mafarki.

Tace:

"Lamarin ya fara ne bayan watanni uku da daukan ciki. Sai nayi mafarki an harbeni a ciki. Tun daga lokacin na fara fuskantar matsala."

Kara karanta wannan

Ina Buƙatar Mijin Aure Cikin Gaggawa, In Ji Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga karshe, Matar da ya dau juna biyu tsawon shekara 6 ta haihu
Daga karshe, Matar da ya dau juna biyu tsawon shekara 6 ta haihu
Asali: Original

Ta kwashe shekaru 3 tana kwana a coci don neman sauki

Taiwo tace bayan shekara daya bata haihu ba, sai aka bata shawaran ta koma rayuwa a cikin coci.

Tace sai da ta kwashe shekaru 3 da watanni shida kafin wani dan'uwanta ya dauketa daga cocin saboda rashin samun haihuwar.

Ta kusa kashe kanta

Taiwo ta bayyana cewa akwai lokutan da cikin ke sauka kamar ba tada ciki kuma akwai lokutan da take jin cikin a bayanta mai maimakon cikinta.

Ta ce har awo da aka yi a asibiti ya nuna cewa babu komai a cikinta.

Taiwo tace lokacin da take zaune a coci, har ta fara shawarar kashe kanta ta hanyar shiga gabar tirela ya murkushe ta.

Ta godewa Allah bisa haihuwa da ta samu.

Kalli bidiyon:

Kara karanta wannan

Ina tsananin bukatar aure cikin gaggawa, Wata Jarumar masana'antar Fim a Najeriya ta cire kunya

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng