Da duminsa: FG ta maka sabon haraji kan kiran waya, ta bayyana amfanin da za a yi da shi

Da duminsa: FG ta maka sabon haraji kan kiran waya, ta bayyana amfanin da za a yi da shi

  • Gwamnatin shugaba Buhari ta kallafawa masu kiran waya sabon haraji ana tsaka da fama da kamfanonin sadarwa yayin da suke yunkurin karin kudin kira
  • Kamar yadda gwannatin ta bayyana, za a yi amfanin da sabon harajin ne wurin daukar nauyin kiwon lafiyar 'yan Najeriya masu rauni
  • Sabuwar dokar Hukumar Inshorar lafiya da shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu ce ta kallafa hakan ga 'yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta kallafa sabon harajin kiran waya a kasar nan domin daukar nauyin kiwon lafiyar masu rauni a Najeriya.

Punch ta ruwaito cewa, wannan ya biyo baya duk da yunkurin da kamfanonin sadarwa suka digan yi a cikin kwanakin nan na kara kudin kira sakamakon halin da suka tsinta kansu a kasar nan.

Da duminsa: FG ta maka sabon haraji kan kiran waya, ta bayyana amfanin da za a yi da shi
Da duminsa: FG ta maka sabon haraji kan kiran waya, ta bayyana amfanin da za a yi da shi. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Harajin wayar na daidai da kobo daya a duk dakika daya kuma yana daga cikin hanyoyin samun kudin da zaa dauka nauyin kiwon lafiya na kyauta ga masu rauni a Najeriya.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

Wamnan na kunshe da sabuwar dokar Inshorar Kiwon lafiya ta 2021 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu a makon da ya gabata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dokar ta hada da tanadin sashi na 26, karamin sashi na 1c wanda ya ce inda za a samo kudin domin kungiyoyi masu raunin ya hada da harajin sadarwa wanda bai gaza kobo daya ba a kowacce dakika na kiran waya.

Kamfanonin sadarwa zasu yi rashin kwastamomi milyan 72 da aka toshewa layukan waya

A wani labari na daban, kamfanonin sadarwa a Najeriya sun shiga mawuyacin hali sakamakon datse layukan waya sama da miliyan 72 a kasar a ranar Litinin, 4 ga watan Afrilun 2022.

A cewar wani kwararre a bangaren sadarwa, umurnin da gwamnatin tarayya ta bayar zai fi shafar kamfanonin sadarwar ne domin za su yi asarar biliyoyin naira ta sanadiyar hakan.

Kara karanta wannan

Yan kasar Nijar, da wasu yan bakin haure ke aikin Okada a Legas, Kwamishanan yan sanda

Kamfanonin sun dogara ne a kan siyar da katin waya don tattara kudaden shiga kuma wannan umurnin babban kalubale ne kai tsaye ga hanyar tattara kudadensu.

An hana kiran waya fita daga layukansu da ba a hada da lambobin NIN ba, kamar yadda gwamnatin Najeriya ta yi umurni.

Masu layukan ba su cike yarjejeniyar wa’adin ranar 31 ga watan Maris da ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zama karkashin Isa Pantami ta diba masu ba. Wata danarwa daga ma’aikatar ta ce kimanin layukan waya miliyan 125 aka hada da lambobin NIN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel