Dalla-dalla: Yadda bene mai hawa 3 ya murkushe jama'a, mutum 4 sun rasu, 5 sun jigata

Dalla-dalla: Yadda bene mai hawa 3 ya murkushe jama'a, mutum 4 sun rasu, 5 sun jigata

  • An tabbatar da mutuwar mutane hudu yayin da wasu biyar suka samu raunuka sanadiyyar rushewar wani bene mai hawa uku a Alayak Lane dake tsibirin Legas
  • Hukumar kwana-kwana ta jihar Legas ta bayyana yadda bene ya rushe sanadiyyar wani mamakon ruwan sama da aka yi a yankin
  • Har yanzu ba a san yawan mutane dake cikin ginin ba, amma ana cigaba da ceto rayukan jama'ar da mummunan lamarin ya ritsa da su

Legas - An tabbatar da mutuwar mutane hudu yayin da wasu mutane biyar suka samu raunuka sanadiyyar rushewar sabon gini a Alayaki lane, dake tsibirin Legas.

An gano yadda bene mai hawa uku da ake ginawa ya rushe yayin da aka yi mamakon ruwan sama a yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Boka ya dirkawa matar aure ciki, rikici ya barke tsakaninsa da mijinta: Ga labarin dalla-dalla

Dalla-dalla: Yadda bene mai hawa 3 ya murkushe jama'a, mutum 4 sun rasu, 5 sun jigata
Dalla-dalla: Yadda bene mai hawa 3 ya murkushe jama'a, mutum 4 sun rasu, 5 sun jigata. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban hukumar kwana-kwana ta Legas, Ibrahim Farinloye ne ya tabbatar da aukuwar lamarin.

"An ceto biyar da ransu tare da hudu matattu. Masu ceton rai na kan hanyarsu," cewarsa.

Babban sakataren hukumar kwana-kwana na jihar, Dr Olufemi Oke-Osanyitolu, ya ce a binciken da aka yi an gano yadda aka yi ginin tare da karya dokokin tsare rayuka.

A cewarsa, "Hukumar ta hanzarta kawo dauki ga lamarin wanda ya riga ya ci karo da dokokin tsare rayuka na gini.
"Bayan cigaba da bincike, an gano yadda masu ginin suka cigaba da aikinsu yawancin lokaci a dare ko karshen makwanni.
"Har yanzu ba a tabbatar da yawan mutanen dake cikin ginin ba. An dai ceto biyar da ransu yayin da aka ga gawar wani sannan ana cigaba da kokarin ganin an ceto rayuka."

Kara karanta wannan

Ana Zaman Ɗar-Ɗar Yayin Da Tsohon Shugaban APC Na Bauchi Ya Mutu Cikin Yanayi Mai Ɗaure Kai

Cikin lokutan nan jihar Legas ta zama babbar cbiyar rushewar gini. Wanda hakan ke lashe rayuka da janyo wa jama'a raunuka.

A kalla mutane 10 sun rasa rayukansu a ranar Lahadi, 1 ga watan Mayu, 2022 yayin da bene mai hawa uku ya ruguzo a Ebute Metta, cikin garin Legas.

Gidan sama hawa 3 ya ruguje a jihar Legas, rayuwaka da dama sun salwanta

A wani labari na daban, ana fargabar mutuwar jama’a da dama bayan wani katafaren gidan sama mai hawa uku ya ruguzo a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wannan gida na lamba ta 24 kan titin Daddy Alaja a unguwar Apongbon na jihar Legas, kuma har zuwa lokacin hada wannan labara, majiyar Legit.ng bata gani musabbabin abin da yayi sanadiyyar ruguzowar gidan ba.

Sai dai an ruwaito ana nan ana gudanar da aikin ceton jama’a, amma duk da haka, jami’an hukumar bada agajin gaggawa na shan wahalar gudanar da ceton.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: