Mutum 56 kacal ke hana ruwa tafiya a Najeriya, Manjo Hamza Al-Mustapha
- Tsohon Soja kuma dan takara kujerar shugaban kasa, Hamza Al-Mustapha ya ce wasu mutane ke cinye arzikin Najeriya
- Al-Mustapha ya shiga jerin masu takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a zaben 2023
- Al-Mustapha yace abun farko da zai yi idan ya samu nasara shine kawo karshen yan ta'addan Boko Haram
Kaduna - Tsohon dogarin marigayi shugaban kasan mulki Soja, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya bayyana cewa wasu mutum 56 ke hana ruwa tafiya a Najeriya.
Al-Mustapha yace wadannan mutane 56 ke cinye arzikin Najeriya.
Ya bayyana cewa lokacin da yake daure, yayinda ake azabtar da shi ya fahimci wadannan mutane 56 kuma idan aka samu nasarar kawar da su, Najeriya za ta samu cigaba.
Al-Mustapha ya bayyana hakan ne yayin hira da sashen Hausa na BBC a jihar Kaduna.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Manjo Hamza Al-Mustapha ya yanki tikitin takara kujerar shugaban kasa a 2023
Hamza Al-Mustapha ya shiga jerin masu neman takara kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Al-Mustapha ya ayyana niyyar takararsa karkashin jam'iyyar Action Alliance AA.
Yayin saya Fam dinsa na takara a hedkwatar jam'iyyar AA dake Abuja ranar Alhamis, jami'in soja mai ritaya ya yi alkawarin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi yankin Arewa maso gabas da Arewa maso yamma.
Manjo Hamza Al-Mustapha, ya ci alwashin karar da 'yan ta'addan Boko Haram, inda yace cikin watanni shida zai yi hakan, domin kuwa dajin Sambisa na jihar Borno zai tare bayan gaje kujerar Buhari domin gane wa kansa hanyar da zai bullowa lamarin.
Sojojin Najeriya sun lalace
Al-Mustapha ya bayyana damuwarsa ga yadda jami'an sojin Najeriya suka zama lalatattu, wadanda basu dauki kishin kasa a matsayin komai ba, inda yace yana da shirin gyara gidan soja, tare da rage wa wasua jami'ai girma idan suka gagara cimma abin da ya daura su a kai.
Asali: Legit.ng