Da dumi: Shugaba buhari ya dira Abu Dhabi, kasar UAE inda yaje ta'aziyya
1 - tsawon mintuna
- Shugaban kasan Najeriya ya tafi kai gaisuwar ta'aziyyya hadaddaiyar daular Larabawa bisa rasuwar shugaban kasansu
- Fadar shugaban kasa ta bayyana muhimmancin wannan tafiya ga alakar dake tsakanin Najeriya da Dubai
- Shugaban kasan zai samu rakiyan wasu Ministocinsa da hadimai makusanta
Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Abu Dhabi don ganawa da Shugaban kasar UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, da daren Alhamis, 19 ga watan Mayu, 2022.
Hadimin sashen gidajen talabijin da rediyo na shugaban kasa, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.
Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi kasar UAE don gaisuwar ta'aziyyar rasuwar tsohon Sarki Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan da ya rasu farkon makon nan.
Buhari ya samu kyakkyawan tarba daga wajen sabon shugaban kasar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng
Tags: