Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe wani kasurgumin kwamandan Boko Haram
- Rahotannin da ke fitowa daga rundunar sojin Najeriya sun bayyana cewa, dakarun soja sun hallaka wasu kasurguman 'yan ta'adda
- Hakazalika, an kama wasu da dama tare da kwato wasu kayayyakin aikata laifi a hannun 'yan ta'addan a jihar Borno
- A halin da ake ciki, rundunar soji ta ce wasu 'yan ta'adda da dama tare da iyalansu sun mika wuya ga rundunar
Abuja - Dakarun sojin Najeriya da ke aiki da Operation Hadin Kai, sun kashe wani kasurgumin kwamandan Boko Haram Abubakar Sarki a dajin Sambisa, da ke Yuwe a karamar hukumar Konduga a jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.
Jami’an rundunar a wani samame na hadin gwiwa da suka kai a lokacin da suke gudanar da aikin share fage, sun kuma kashe Amir kuma shugaban yankin Gaita na 'yan ta'addan, Malam Shehu da wasu dakarunsa.
Kakakin rundunar soji, Maj.-Gen. Benard Onyeuko ne ya bayyana hakan ga manema labarai a hedikwatar tsaro da ke Abuja yayin da yake bayar da bayanai kan nasarorin da sojojin suka samu a fadin kasar tsakanin 28 ga Afrilu zuwa 19 ga Mayu 2022.
Onyeuko, ya kuma bayyana cewa, ya zuwa ranar 16 ga Mayu, 2022, jimillar ‘yan ta’addar Boko Haram 1,627 da iyalansu da suka hada da maza 331, mata 441 da kananan yara 855 sun mika wuya ga sojoji a wurare daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake karin haske, babban jami’in sojan ya bayyana cewa sojojin sun kama Mallam Modu Goni, wani dan ta’adda da ke sayar da kayayyaki ga 'yan ta'adda a Kasuwar Bunin Yadi bisa wani rahoton sirri.
Hakazalika, rundunar ta bayyana kayayyakin da ta kwato da suka hada da makamai, kayan abinci da kudade.
El-Rufai: Ƴan Boko Haram Da ISWAP Sun Yada Zango a Ƙananan Hukumomi 2 a Kaduna
A bangare guda, Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana damuwarta akan yadda kungiyoyin ta’addanci su ke ta aiwatar da harkokinsu a cikin jihar, Channels TV ta ruwaito.
Yayin gabatar da rahotannin watanni hudu na farkon shekarar 2022 ga majalisar tsaron jihar, Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan ya ce yan kungiyar Ansaru da Boko Haram sun baje kolin ta’addancinsu a Birnin Gwari da karamar hukumar Giwa.
Aruwan ya ce wasu ‘yan ta’adda sun fara jan ra’ayin mazauna kauyaku da kyautuka yayin da su ke horar da su akan ta’addanci.
A wani labarin, a yau ne shugaban 'yan ta'addan Boko Haram Abubakar Shekau ke cika shekara guda da barin duniya, tun bayan da rahotanni suka ce ya sheke kansa a wani artabu da 'yan uwansa 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan ISWAP ne.
Boko Haram dai kungiya ce ta ta'addanci da ta shahara a Najeriya da kasashen nahiyar Afrika makwabta, inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma salwantar dukiyoyi da ababen more rayuwa.
An san kungiyar da kai hare-hare kan ababen gwamnati, daidaikun jama'a har ma da wuraren ibada da makarantu.
Asali: Legit.ng