Hoton miji da mata sun kammala digirin digirgir daga jami'a daya, sun karba satifiket tare

Hoton miji da mata sun kammala digirin digirgir daga jami'a daya, sun karba satifiket tare

  • Wani mutum ya bada labarin yadda shi da matarsa su ka yi karatu tare sannan suka kammala cikin matsanancin farin ciki
  • A halin yanzu, sun karbi takardun digirinsu na uku a rana daya daga jami'a daya a kasar Amurka
  • Su biyun, Tariful Islam da matarsa Farhana sun kammala karatunsu daga jami'ar Texas Technology, sannan sun saki zuka-zukan hotunansu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Amurka - A halin yanzu, Tariful Islam da matarsa Farhana na cikin matsanancin farin ciki saboda yadda suka amsa takardar shaidar kammala digirinsu na uku a rana daya daga makaranta daya.

Su biyun sun amsa takardar shaidar kammala karatunsu daga jami'ar Texas Technology dake Amurka.

Hoton miji da mata sun kammala digirin digirgir daga jami'a daya, sun karba satifiket tare
Hoton miji da mata sun kammala digirin digirgir daga jami'a daya, sun karba satifiket tare. Hoto daga LinkedIn/Tariful Islam
Asali: UGC

Ma'auratan biyun sun wallafa zuka-zukan hotunansu don murnar babbar nasarar da suka samu duk da labarinsu ya yi yawo saboda yadda yake da ban sha'awa.

Kara karanta wannan

Matata Da ƳaƳana Sun Saba Haɗuwa Su Lakaɗa Min Duka, Magidanci Mai Neman Saki

Yayin bada labarin abubuwan da suka kai su ga nasara, Islam ya rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A shekarar 2006: mun fara karatun digirinmu na farko a Biotechnology & Genetic Engineering Discipline a jami'ar Khulna, ta Khulna dake Bangladesh.
2010: Mun kammala karatu tare
2010: Na fara aiki da wani kamfanin hada magunguna
2011: Mun yi aure (Alhamdulillah)
2015: An albarkacemu da 'diya mace (Alhamdulillah)
2017: Na fara digirina na uku a kasar Japan. Rayuwa tai min kunci saboda rashin matata da 'diyata. Na takura matuka. Hakan yasa na fara neman wasu jami'oin.
2018: Farhana ta fara digirinta na uku tare matsayin RA a fannin Biology, a jami'ar Texas Tech. Ta tafi da 'diyarmu.
2018: Na fara digirina na uku a kyauta a matsayin TA a fannin Nutritional Sciences a jami'ar Texas.
2020: Annoba ta barke! Mu biyun duka muksakammala jarabawar cancantar fara digiri na uku.

Kara karanta wannan

Taron siyasa a Plateau: Atiku ya ba da hakuri bisa fatattakar 'yan jarida da ya yi

2021: Aka albarkace mu da 'diyarmu ta biyu (Alhamdulillah)
2022: Cikin nasarar muka kare karatunmu, gami da amsar kwalin digirinmu na uku !"

Chaarmaine Lane ya ce:

"Kawai abun da ya birge ni shi ne yadda dukkanku ku ka hada kai ku ka yi komai tare. Dukkan kalubalen da ku ka fuskanta ya kamata a ce ya nisantar daku daga juna, amma sai ya kara muku kusanci. Wannan shi ne ke nuna asalin mene ne aure, kun zama tsoka daya. Tariful Islam ina taya ka murna tare da kyakyawar matarka!!"

Chioma Jou Okonkwo tayi tsokaci:

"Ina tayaka murna tare da matarka. Labarin ku abun kara karfin guiwa ne musamman ga ma'auratan da ke neman daidaito tsakanin karatu da rayuwar iyali. Na yi farin ciki da yadda ku biyun duka ku ka yi nasara daga karshe."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: