Tsohon zakaran kwallon Afrika, Patrick Mboma, ya musulunta kuma kai tsaye aka aura masa amarya

Tsohon zakaran kwallon Afrika, Patrick Mboma, ya musulunta kuma kai tsaye aka aura masa amarya

  • Shahrarren dan kwallon Kamaru, Patrick Mboma, ya karbi shahadar shiga Musulunci ranar Juma'a
  • Shigarsa Musulunci ke da wuya aka gwangwajeshi da sabuwar kyakkyawar amarya, Fatoumata Binta
  • Mboma ne mutum mafi kwallaye a tarihin kwallon kasar Kamaru, fiye da Samuel Eto'o

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon tauraron dan kwallon nahiyar Afrika kuma na kasar Kamaru, Patrick Mboma, ya Musulunta ranar Juma'a da ta gabata a Masallacin Bonamosadi dake Douala.

Bayan komawarsa addinin Musulunci, ya mayar da sunansa Abdoul Djalil Mboma.

A bidiyon da ya yadu a kafafen ra'ayi da sada zumunta, Mboma ya karbi shahada a Masallaci.

Shi da kansa kuma ya daura bidiyo a shafinsa na Instagram.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mboma, dan shekara 51 ne dan kwallon kasar Kamaru da yafi zura kwallaye a tarihin kasar.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

Gabanin ritayarsa daga kwallo a Mayun 2005, ya bugawa kungoyi a Turai irisnu Châteauroux, Paris Saint-Germain, Metz, Gamba Osaka, Cagliari, Parma, Sunderland, Al-Ittihad, Tokyo Verdy, da Vissel Kobe.

Ya taka leda a gasar kofin duniya ta 1998 da 2022 kuma ya jagoranci Kamaru wajen cin gasar kofin nahiyar Afrika a 2000 da 2002.

A 2000, an alantasa matsayin zakarar dan kwallon nahiyar Afirka.

An gwangwajeshi da sabuwar amarya

Jim kadan aka daura masa aure, AbdulJalili Mboma ya auri diya Musulma yar kasar Guinea mai suna Fatoumata Binta.

Patrick Mboma
Tsohon zakaran kwallon Afrika, Patrick Mboma, ya musulunta kuma kai tsaye aka aura masa amarya Hoto: @EkwatTV
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng