Yanzu-yanzu: An saki sakamakon jarabawar JAMB a Najeriya
- Bayan mako daya da zana jarabawar, hukumar JAMB ta saki sakamakon jarabawar bana da dalibai suka zana
- Hukumar ta bayyana cewa hanya daya kacal za'a iya bi wajen duba sakamakon saboda tsaro daga yan damfara
- Dubunnan daruruwan dalibai da suka kammala karatun sakandarensu sun zana wannan jarabawa
Abuja - Hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'in Najeriya watau JAMB ta sanar da sakin sakamakon jarabawar bana 2022 da dalibai a fadin tarayya suka zana.
Shugaban sashen hulda da jama'a na JAMB, Fabian Benjamin, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, rahoton TheNation.
Ya bayyanawa dalibai da suka zana jarabawar cewa za su iya duba sakamakonsu a wayoyinsu na tarho.
A cewarsa, su tura sakon akwatin SMS 'UTMERESULT zuwa 55019 a wayar da aka musu amfani wajen rijista.
A cewar jawabin:
"Don duba sakamakon UTME, abinda kowani dalibi ke bukatan yi shine tura UTMERESULT zuwa 55019 da lambar wayar da akayi amfani wajen rijista, za'a turo musu sakamakon."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Wannan shine hanya daya tilo da aka samar don duba sakamakon a yanzu don wasu dalilai."
2023: Zan soke JAMB, WAEC da NECO saboda kowa ya je makaranta inji ‘Dan takaran APC
Adamu Garba II wanda yana cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya bayyana yadda zai bunkasa harkar ilmi a Najeriya.
Adamu Garba II ya yi bayani a shafinsa na Facebook, ya ce idan ya karbi mulkin kasar nan, zai ba kowa damar zuwa makarantu na gaba da sakandare.
Matashin ‘dan siyasar zai cin ma wannan buri ne ta hanyar ruguza hukumomin WAEC, NECO da JAMB da su ke shirya jarrabawan kammala sakandare.
Kamar yadda yake bayani, Garba II zai kawo tsari ta yadda duk wanda ya yi nasara a makarantun firamare da sakandare, zai iya zuwa mataki na gaba.
Asali: Legit.ng