Tashin Hankali: Wani Bam ya sake tashi a gidan giya a jihar Kogi, mutane sun mutu

Tashin Hankali: Wani Bam ya sake tashi a gidan giya a jihar Kogi, mutane sun mutu

  • Wani abun fashewa da mutane ke zaton Bam ne ya tashi a wata mashaya da ke Kabba, jihar Kogi ranar Laraba da daddare
  • Wasu mazauna yankin da suka garzaya wurin gane wa ido sun ce mutum uku ne suka mutu wasu kuma na kwance a Asibiti
  • Kwamishinan yan sanda na Kogi ya ce rahoton da suka haɗa ya nuna tukunyar Gas ce ta fashe ba Bam ba

Kogi - Akalla mutum uku ake fargabar sun rasa rayuwarsu kuma wasu da dama suka jikkata yayin da wani Bam ya tashi a Kabba, jihar Kogi da daren ranar Laraba.

Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9:45 na dare lokacin da mutane ke tsaka holewarsu a wani gidan Giya.

Taswirar jihar Kogi.
Tashin Hankali: Wani Bam ya sake tashi a gidan giya a jihar Kogi, mutane sun mutu Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wata majiya ta bayyana cewa:

"Na ji wata ƙara mai tsananin ƙarfi kuma babu nisa daga inda nake, nan take na nufi wurin dom gane wa idona, na ga gawar mutum uku kwance yayin da waɗan da suka jikkata an kai su Asibiti."

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

"Mutanen da suka ji rauni an kai su babban Asibitin St. John da ke Kabba, domin ba su kulawa."

Haka nan, wani ɗan Acaba wanda ya bayyana sunansa da Dele, ya ce: "Bam ne ya tashi saboda ƙarar ta yi tsanani, mutane sun mutu, wasu sun jikkata. Na ga yadda jami'an tsaro suka ɗauki mutanen zuwa Asibiti a Kabba."

Wane matakin jami'an tsaro suka ɗauka?

Sai dai kwamishinan yan sanda reshen Kogi, Mista Edward Egbuka, ya shaida wa hukumar dillancin labarai NAN cewa rahoton da suka samu ya nuna tukunyar Gas ce ta fashe ba Bom ba.

Ya ƙara cewa a halin yanzun Jami'ansa na aiki kan lamarin kuma zai fitar da cikakken bayani game da fashewar bayan kammala bincike.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa irin wannan harin ya faru a jihar Taraba a watan da ya gabata, kuma daga bayan kungiyar ISWAP ta ɗauki nauyin kai harin.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

A wani labarin kuma Hukumar sojojin Najeriya ta kama wani Soja dake siyarwa yan bindiga makamai a Zamfara

Hukumar sojojin Najeriya ta kama wani Soja dake sayarwa yan bindiga makamai da kayan sojoji a jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama sojan ne yana shirin sayar da Alburusai 1,000 kan kudi Naira miliyan ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: