Za'a yi ambaliya a jihohi 32 bana, Ministan Ruwa ya lissafo su

Za'a yi ambaliya a jihohi 32 bana, Ministan Ruwa ya lissafo su

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana wuraren da ake sa ran fuskantar Ambaliyar ruwan sama a shekarar 2022
  • Ministan ruwa a baya ya bayyana cewa ba'a son abinda ya faru a 2012 ya maimaita kansa a kasar nan
  • Kananan hukumomi 445 a Jihohin Najeriya 32 ake hasashen zasu fuskanci ambaliya bana

Abuja - Kimanin kananan hukumomi 445 a fadin jihohi 32 da birnin tarayya Abuja zasu fuskanci ambaliyar ruwan sama bana, Ministan ruwa, Injinya Suleiman Adamu ya bayyana.

Ministan ya lissafa wadannan jihohi a taron gabatar da rahoton hasashen ambaliya na shekara-shekara na hukumar ayyukan ruwa a Najeriya (NIHSA), rahoton TheNation.

Ya bayyana cewa kananan hukumomi 233 zasu fuskanci ambaliya mai tsanani yayinda kananan hukumomi 212 zasu fuskanci ambaliya mara tsanani bana.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Jihohin da zasu fuskanci ambaliya mai munin gaske a cewarsa sun hada da Lagos, Edo, Delta, Delta, Akwa Ibom, Abia da birnin tarayya Abuja.

A jihar Rivers, Bayelsa, Cross River, Delta, Edo, Lagos, Ogun da Imo, ya ce za'ayi ambaliya ne saboda tekunansu sun cika kuma hakan zai shafi harkar masunta.

Tsawon watanni nawa za'a fuskan ambaliyar?

Ministan ya kara da cewa kananan hukumomi 57 zasu fuskanci nasu ambaliyar tsakanin watan Afrilu da Yuni, yayinda sauran 220 zasu fuskanci nasu tsakanin Yuli da Satumba.

Daga biranen da zasu fuskanci wannan ambaliya bana a cewarsa sune Lagos, Kaduna, Suleja, Gombe, Asaba, Port Harcourt, Benin da Lokoja.

Za'a yi ambaliya a jihohi 32 bana, Ministan Ruwa ya lissafo su
Za'a yi ambaliya a jihohi 32 bana, Ministan Ruwa ya lissafo su
Asali: UGC

A bara, Ministan ya yi hasashen mumunan ambaliyar ruwan sama a jihohin Najeriya akalla 28.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Inuwa Yahaya ya lamuncewa Kayode Fayemi don ya gaji shugaba Buhari

Jihohin da aka lissafo sune,Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, FCT, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano and Kebbi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba da Zamfara.

Ministan ya ce saboda haka suka shirya don ankarar da yan Najeriya kan abinda ka iya faruwa.

Ya yi kira ga yan Najeriya su taimakawa wadanda wannan iftila'i ya fadama wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: