Karo na uku Malam Abduljabar Kabara ya sake watsi da Lauyoyinsa

Karo na uku Malam Abduljabar Kabara ya sake watsi da Lauyoyinsa

  • Malamin addini, Sheikh Abduljabbar, ya bukaci kotu ta bashi dama ya cigaba da kare kansa maimakon lauyoyi
  • Sheikh Abduljabbar yace ya sallami lauyoyinsa saboda sun gaza kuma suna ikirarin cewa ana musu barazana
  • Alkali ya bukaci majalisar taimakawa marasa kafi ta baiwa Malam AbdulJabar lauya kyauta don tsaya masa

Kano - A karo na uku, shahrarren Malamin dake tsare a gidan gyara hali, Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya sake watsi da Lauyoyinsa

Malam Abduljabbar kamar yadda ya yiwa Lauyoyinsa na baya, yana zarginsu da gaza kare shi a gaban Kotu, rahoton Arewa Radio.

AbdulJabbar ya bukaci kotu ta rabu da shi zai iya cigaba da kare kansa, tunda duk lauyan da ya dauka sai ya ce ana yi masa barazana da rayuwarsa.

Su kuwa lauyoyin gwamnatin jihar sun bukaci kotun ta umurci hukumar dake baiwa marasa karfi kariya a kotu kyauta, watau Legal Aid Council da ta bawa Malamin lauyan.

Kara karanta wannan

Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa

A karshe, kotun ta amince da hakan kuma ta yi umarni ga Legal Aid Council ta bawa Abduljabar Lauyoyin da za su kare shi.

An dage zaman zuwa ranar 26 ga Mayu, 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malam Abduljabar Kabara
Karo na uku Malam Abduljabar Kabara ya sake watsi da Lauyoyinsa Hoto: Arewa Radio 93.1
Asali: Facebook

AbdulJabbar ya gabatar da litattafai 27 a kotu, ya rantse da Al-Qur'ani bai zagi Annabi ba

Sheikh Abduljabbar Nasiru-Kabara, ya fara gabatar da nasa hujjojin gaban kotu a shari'ar dake gudana tsakaninsa da gwamnatin jihar Kano.

AbdulJabbar ya gabatar da litattafai 27, ciki akwai Almuhadisu Alfasil Banul Rawawil Wali, Sunannun Darumi, Jami’u Ilmi, Tauhiful Afkar, Anannakatu Almukaddimatu Ibn Salah, Al Gaya, dss.

A baya mun ruwaito cewa an shigar da Malam AbdulJabbar kotu bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Gabanin fara jawabinsa yau a kotu, AbdulJabbar ya rantse da Alqur'ani mai girma cewa bai zagi Annabi ba, rahoton NAN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng