Jerin Ministocin 9 da Shugaba Buhari ya yiwa umurni suyi murabus nan da kwanaki 5

Jerin Ministocin 9 da Shugaba Buhari ya yiwa umurni suyi murabus nan da kwanaki 5

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci dukkan ministocinsa da ke son yin takara a zaben 2023 da ke tafe su mika takardan murabus dinsu kafin ko ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022.

Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Villa a Abuja.

Legit ta tattaro muku jerin Ministocin da suka ayyana niyyar takarar kujeran mulki.

Yayinda shida (6) suke son zama shugabannin kasa, biyu (2) na son zama gwamnonin jihohinsu kuma daya (1) na son zama Sanata.

Shugaba Buhari
Jerin Ministocin 9 da Shugaba Buhari ya yiwa umurni suyi murabus nan da kwanaki 5 Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP

Ga jerinsu:

  1. Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi (Mai neman kujeran shugaban kasa)
  2. Ministan Niger Delta, Godswill Akpabio; (Mai neman kujeran shugaban kasa)
  3. Minister kwadago, Chris Ngige; (Mai neman kujeran shugaban kasa)
  4. Minister Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu (Mai neman kujeran shugaban kasa)
  5. Karamin Ministan Ilmi, Emeka Nwajiuba(Mai neman kujeran shugaban kasa)
  6. Karamin Ministan Man fetur, Timipre Sylva(Mai neman kujeran shugaban kasa)
  7. Karamin Ministan Ma'adinai da karafuna, Uche Ogar (Mai neman kujeran gwamnan jihar Abia)
  8. Ministar harkokin mata, Pauline Tallen (Mai neman kujeran Sanata)
  9. Ministan Shari'a, AGF Abubakar Malami (Mai neman kujeran gwamnan jihar Kebbi)

Karamin Ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, ya yi murabus

Karamin Ministan Ilmi Emeka Nwajuiba ya zama mutumin farko da yabi umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Emeka Nwajuiba ya yi murabus daga kujerarsa ta Minista ne domin maida hankali kan yakin neman zaben zama shugaban kasa

Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya bayyana hakan a zaman majalisar zartaswar ya gudana ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng